Kotu Ta Bada Belin Abba Kyari Bayan Shafe Wata 18 A Gidan Gyaran Hali

Kotu Ta Bada Belin Abba Kyari Bayan Shafe Wata 18 A Gidan Gyaran Hali

FCT Abuja - Babban Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta bada belin dakataccen Mataimakin Kwamishinan Yan Sanda, DCP, Abba Kyari.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Mai shari'a Kolawole Omotosho ne ya bada balin dan sandan a ranar Alhamis bayan ya shafe wata 18 tsare a gidan gyaran hali, rahoton The Punch.

Alkali ya bada belin Abba Kyari
Abba Kyari ya samu beli bayan shafe watanni 18 a gidan gyaran hali. Hoto: Channels TV
Asali: Facebook

Hukumar Yaki da Masu Fatauci da Shan Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta ayyana neman Kyari ruwa a jallo kan zarginsa da hannu a badakalar hodar iblis mai nauyin kilogiram 25.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hujjar bada belin Abba Kyari

Mai shari'a Omotosho ya ce duba da cewa Kyari da tawagarsa sun ki tserewa a lokacin da aka kai hari gidan yarin Kuje, inda kimanin kashi 90 na fursunoni suka tsere ya nuna cewa Kyari a shirye yake ya fuskanci zargin da ake masa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Bayar Da Belin Abba Kyari Kan Kudi Naira Miliyan 50

Alkalin ya kara da cewa zargin da ake yi wa Kyari ba su kai girman a hana shi beli ba kuma ba a fargabar zai shiga jirgin sama ya tsere daga kasar, Channels TV ta rahoto.

Daga bisani an kama shi a watan Fabrairun 2022 bayan NDLEA ta yi zargin cewa ya taba wasu kwayoyi da aka kwato a matsayin hujja daga wadanda ake zargi da laifi kuma aka tsare shi a gidan gyaran hali na Kuje.

Amma, har yanzu akwai shari'ar da ake yi da Kyari a gaban Mai Shari'a Emeka Nwite na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja.

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel