Jihar Zamfara
Fitaccen lauya, Bulama Bukarti ya kaddamar da asusun tallafawa sojojin da suka hallaka Halilu Sabubu domin nunawa sojojin yan Najeriya suna tare da su.
An samu asarar rayuka a jihar Zamfara bayan wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji ya kife a jihar Zamfara. Hatsarin jirgin ya ritsa da fasinjoji masu yawan gaske.
Malamin Musulunci, Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya tura sako ga Bello Turji da sauran yan ta'adda bayan kisan Halilu Sabubu da safiyar ranar Juma'a.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wasu daga cikin 'yan bindigan da suka kashe Sarkin Gobir. Sojojin sun sheke uku daga cikin miyagun har lahira.
Hafsan tsaron kasar, Janar Christopher Musa ya ba da kyautar kudi ga dakarun sojoji da suka yi nasarar hallaka dan ta'adda, Halilu Sabubu a Zamfara a jiya Juma'a.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba kan nasarorin da dakarun sojoji suka samu kan 'yan bindiga. Ya yaba kan kisan da aka yiwa Halilu Buzu Sububu.
Kwanaki uku kafin hallaka rikakken dan ta'adda, Halilu Sabubu, an wallafa faifan bidiyo inda ya ke rokon yan uwansa kan lamarin tsaro ciki har da Bello Turji.
Ta’adin Halilu Sabubu Buzu ya zo karshe domin sojoji sun hallaka shi, tun a watannin baya aka ji jami’an tsaro su na cigiyar Halilu Buzu domin a kashe shi.
Gawurtaccen ɗan bindigar nan, Bello Turji ya yi magana kan tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isah Pantami, ya ce yana da wazinsa da ya ji yana kafirta gwamnati.
Jihar Zamfara
Samu kari