Zamfara: ‘Yan Daba Sun Lakadawa Shugaban ‘Yan Jarida Mugun Duka, Sun yi Barazana ga Jami’ai

Zamfara: ‘Yan Daba Sun Lakadawa Shugaban ‘Yan Jarida Mugun Duka, Sun yi Barazana ga Jami’ai

  • Wasu matasa da ake zargin ‘yan daba ne sun lakadawa shugaban kungiyar ‘yan jarida na jihar Zamfara mugun duka a sakateriyar kungiyar dake Gusau
  • An gano cewa, shugaban ya bukaci ‘yan daban da su bar shagon da suka kama na kamfen a sakateriyar gudun hargitsin da zasu iya janyowa
  • Sai dai ko bayan zuwan ‘yan sanda, ‘yan daban sun ce ba zasu tashi ba kuma zasu halaka duk wanda yace su tashi tare da hana ‘yan jarida aikinsu a jihar baki daya

Zamfara - Wasu da ake zargin ‘yan daba ne a ranar Alhamis sun lakadawa shugaban ‘yan jaridan jihar Zamfara, Kwamared Ibrahim Maizare mugun duka tare da yin barazanar cin zarafin duk manema labaran dake aiki a jihar.

Kara karanta wannan

Dakarun MNJTF Sun Kama Mutum 40 da Buhu 364 na Wake, 102 na Masara Zasu Kai wa ‘Yan ISWAP

Taswirar Zamfara
Zamfara: ‘Yan Daba Sun Lakadawa Shugaban ‘Yan Jarida Mugun Duka, Sun yi Barazana ga Jami’ai. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

‘Yan daban sun fada shugaban ‘yan jaridan da suka ne bayan ya bukaci wasu ma’aikata dake gyaran wani shago a sakateriyar ‘yan jaridan da za a yi amfani da shi don kamfen da su tsaya da aikinsu, Channels TV ta rahoto hakan.

‘Yan daban sun ce ba zasu daina aikin ba ko kuma su bar wurin saboda ‘dan siyasa ne ya basu wurin kuma matukar yana numfashi ba zasu bar wurin ba.

Tun farko NUJ ta bada hayar shagon inda ake siyar da abinci amma daga bisani mai siyar da abincin Ta Tashi daga shagon sai aka mayar dashi ofishin kamfen wanda ‘yan daba ke zuwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wasu ‘yan daba abokan hamayyar wadanda ke amfani da shagon sun banka masa wuta a shekarar 2021 kuma NUJ ta bukace ‘yan daban da su tattara su bar shagon saboda tsoron kada wata rana a kone dukkan ginin.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Bindige Masu Garkuwa da Mutane 2, Sun Samo Kudin Fansa N8.4m a Bauchi

Ko bayan ‘yan sanda sun isa sakateriyar, ‘yan daban sun cigaba da kunduma zagi kan jami’an da sauran mambobin kungiyar, lamarin da yasa ‘yan sanda suka hanzarta barin wurin.

A yayin martani jim kadan bayan faruwar lamarin, sakataren kungiyar, Kwamared Ibrahim Ahmad Gada ya bukaci hukumomin tsaro da su bai wa rayuka da kadarorin ‘yan jaridar dake jihar kariyaw inda ya kara da cewa rayukan ‘yan jarida a jihar na cikin babban hatsari.

“Bayan isar ‘yan sanda wurin, sun bayyana kai tsaye cewa babu wanda ya isa ya hana su lamurransu a wurin kuma sun shirya cin zarafi ko halaka duk wani ‘dan jaridan da ke jin sai sun bar wurin.”

- Gada yace.

“Muna kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su kawo mana dauki, kungiyar ‘yan jarida da dukkan ‘yan jaridan dake jihar Zamfara na fuskantar barazana a kan rayuwarsu.
“Hukumomin tsaro su fahimci halin da muke ciki saboda idan babu zaman lafiya, ba zamu iya aiki ba.”

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Kai Har Asibitin Abdulsalami Abubakar, Sun Sheke Mutum 2 Tare da Sace Wasu

- Ya kara da cewa.

ISWAP Sun Fara Kafa Sansanoninsu a Yankunan Zamfara, Gwamnatin Jiha ta Koka

A wani labari na daban, mambobin kungiyar ISWAP an gano suna kafa sansanoni a wuraren kauyen Mutu dake yankin Mada ta karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara.

Daily Trust ta rahoto cewa, kwamitin gurfanarwa na laifukan da suka hada da ‘yan bindiga da mambobin kwamitin tsaro da sirri, Dr Sani Shinkafi ya bayyana hakan a wani taro a Gusau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel