Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara Ahmad Sani Ya Rasu

Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara Ahmad Sani Ya Rasu

  • Yanzu muke samun mummunan labarin rasuwar shugaban jam'iyyar PDP na jihar Zamfara, Ahmad Sani Kaura
  • Rahotanni sun bayyana cewa, ya rasu ne yayin da ya halarci wani taron zaman lafiya kan zaben 2023 mai zuwa a Gusau
  • An zabi Kaura da mataimakinsa a watan Satumban bana da nufin su rike PDP a Zamfara na tsawon shekaru uku

Gusau, Zamfara - Shugaban jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Zamfara, Ahmad Sani Kaura ya riga mu gidan gaskiya, Channels Tv ta ruwaito.

An ruwaito cewa, ya yanki jiki ya fadi ne a ranar Laraba a Gusau yayin wani taron zaman lafiya da aka gudanar da majalisar Ulama kan zaben 2023 mai zuwa.

Shugaban PDP na Zamfara ya riga mu gidan gaskiya
Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara Ahmad Sani Ya Rasu | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Jigon na PDP a jihar, Aminu Umar ya bayyana cewa, Kaura ya kasance ba shi da lafiya, kuma bai murmure ba lokacin da ya halarci wannan zama.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Atiku ya samu nakasu a Sokoto, manyan jiga-jigai sun koma APC

Yaushe Kaura ya zama shugaban PDP?

Rasuwarsa na zuwa ne kasa da watanni biyu bayan da aka zabe shi ya zama shugaban PDP a jihar ta Zamfara, Sahara Reporters ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Idan baku manta ba, an zabi Kaura ne da mataimakinsa a watan Satumban bana domin ci gaba da kula da lamurran PDP na tsawon shekaru uku a Zamfara.

Jarida Tribune Online ta ruwaito cewa, za a yi jana'izarsa a garinsu da ke yankin Kaura Namoda bisa tsarin addinin Islama.

Ya zuwa yanzu dai jam'iyyar PDP bata fitar da wata sanarwa ta ta'aziyya ko jaje ba.

Hakazalika, ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance na bayyana rasuwan wannan jigon nata ba.

Mbazulike Amechi, Ministan Sufurin Jiragen Sama Na Farko a Najeriya, Ya Rasu

A wani labarin, ministan farko na ma'aikatar sufurin jiragen sama a Najeriya, Cif Mbazulike Amechi ya riga mu gidan gaskiya, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

2023: Atiku ya yi nadi mai muhimmanci, ya ba wani dan Katsina mukamin babban sakatare

A cewar wata majiyar dangi daga bakin Ezeana Tagbo Amechi na karamar hukumar Nnewi ta Kudu a jihar Anambra, tsohon dan siyasar ya rasu ne a yau Talata 1 ga watan Nuwamba da sanyin safiya.

Rahotannin da muke samu sun bayyana cewa, jigon na Kudu shine mutum na karshe da ya saura a tafiyar Zikist, kuma ya zama minista ne a lokacin yana da shekaru 29, ya rasu yana da shekaru 93.

Asali: Legit.ng

Online view pixel