Siyasar Najeriya
Biyo bayan umarnin Shugaba Tinubu, manyan ministoci hudu da shugabannin hukumomin tarayya sun yi murabus domin tsayawa takarar Gwamna da Sanata a zaben 2027.
A labarin n an, Femi Fani Kayode, jigo a APC ya gano irin matsalolin da za su hana ADC cimma manufar kawar da gwamnatin APC a yayin zaben 2027 mai zuwa.
Masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a jihar Katsina sun goyi bayan Yusuf Buhari ya yi takarar majalisar wakilai a zaben 2027. Sun goyi bayan Dikko Radda.
Gwamnoni da 'yan majalisar APC sun fara kira da a ba su tikitin takara kai tsaye yayin da wasu gwamnonin da suka gama suke neman tikitin takarar Sanata.
Kungiyar Afenifere ta bayyana jam’iyyar SDP a matsayin wadda za ta marawa baya a zaben 2027, yayin da kungiyar ACF ta fayyace matsayinta na mai sanya ido kawai yau.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta sanar da cire sunayen shugabannin jam'iyyar hadaka ta ADC daga shafinta saboda wani kara da aka shigar a kotu a Abuja.
Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta fito ta nuna yatsa ga gwamnatin APC mai mulki a Najeriya. Ta zarge ta da yunkurin shirya mata bita da kulli.
Wani rahoto ya nuna cewa rashin bai wa Peter Obi tikitin takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar ADC na iya tarwatsa 'Obidients' da rage wa hamayya ƙarfi a zaɓen 2027.
Ministan Sufuri, Sanata Sa’idu Alkali, ya yi murabus daga gwamnatin Shugaba Tinubu yau Talata domin tsayawa takarar gwamnan jihar Gombe a babban zaɓen 2027.
Siyasar Najeriya
Samu kari