Sheikh Ahmed Gumi
Sheikh Ahmad Gumi ya ce kashe biliyoyin naira wajen siyo makaman da aka yi su a Yakin Duniya II don yaki da 'yan ta'adda tsohon yayi ne. Ya nemi a tattauna da su.
Cocin Cherubim da Seraphim a jihar Kaduna ya karrama Sheikh Ahmad Gumi da Fasto Yuhanna Buru a matsayin Jakadun zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.
Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud ya ce kashe mutane da ake yi a Kaduna ba kuskure ba ne. Shi ma Dr. Sani Umar Rijiyar Lemu ya fitar da jawabi bayan abin da ya faru.
Tukur Sani Jangebe ya yi wa Bello Matawalle addu’ar samun nasara a zaben gwamna da za ayi a wasu garuruwan Zamfara wanda hakan ya fusata Gwamna mai-ci, Dauda Lawal.
Rigimar siyasar da ke tsakanin Bello Matawalle da Dauda Lawal ya shafi Shehin malami. Tukur Sani Jangebe ya ajiye limancin Juma’a saboda rigimar Zamfara.
Fitaccen mawakin Hausa Shu'aibu Ahmed Abbas, wanda aka fi sani da Lilin Baba ya ziyarci malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi. Ya ba da gudunmawa ga yan gaza.
Femi Fani Kayode ya ce abin da Gumi ya fada game da Nyesom Wike za su hargitsa kasar nan da yaki, sai an taka masa burki. Sadaukin Shinkaffi ya yi wa malamin raddi.
Kungiyar kare hakkin Musulmi ta MURIC ta bayyana cewa yawancin wadanda ke mayarwa Sheikh Ahmad Gumi kan Nyesom Wike basu duba zahirin gaskiya ba.
Mai fafutukar kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho ya gargadi Sheikh Gumi kan kalamansa na nade-nade a wannan gwamnati inda ya ce malamin a yanzu ba shi da ta cewa.
Sheikh Ahmed Gumi
Samu kari