Sheikh Gumi Ya Kawo Hanyar Magance Matsalar 'Yan Bindiga Cikin Sauki

Sheikh Gumi Ya Kawo Hanyar Magance Matsalar 'Yan Bindiga Cikin Sauki

  • Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya nuna kuskuren da sojoji ke yi wajen kawo ƙarshen ƴan bindiga
  • Malamin addinin musuluncin ya yi nuni da cewa ƙarfin da sojojin ke amfani da shi ya wuce ƙima kan miyagun da suka addabi jama'a
  • A cewarsa hare-haren da sojoji ke kaiwa ta ƙasa da ta sama na shafar iyalan ƴan bindigan wanda hakan ke ƙara harzuƙa su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Sanannen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce sojojin Najeriya suna tsawwalawa a hanyar da suke bi wajen yaƙi da ƴan bindiga.

Ya ce hanyar da sojojin ke bi domin kawo ƙarshen ƴan bindigan a yankin Arewacin Najeriya, ta yi tsauri da yawa.

Kara karanta wannan

Kisan sojoji a Delta: Daga karshe an fadi dalilin da ya sa aka kashe jami'an tsaron

Sheikh Gumi ya yi magana kan rashin tsaro
Sheikh Gumi ya nuna cewa sojoji suna tsawwalawa wajen yaki da 'yan bindiga Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Asali: Facebook

Ya ce dakarun sojoji da na sama sun ƙaddamar da hare-hare ta ƙasa da ta sama da suka hallaka iyalan ƴan bindigan, mata da ƴaƴansu, lamarin da ya harzuƙa su, inda suke ganin hakan a matsayin yaƙi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya bayyana hakan ne a wani shiri a shafin X da jaridar Daily Trust ta shirya.

Wace hanya za a magance ƴan bindiga?

Ya dage da cewa bin hanyar amfani da tattaunawa ce kawai za ta dakatar da ayyukan ƴan bindiga a yankin Arewa.

A kalamansa:

“A gare su (sojoji) suna yaƙi ne. Maganar gaskiya sojoji sun tsaurara a kansu, sojojin sama suna kashe iyalansu."

Gumi, wanda a baya ya sha shiga daji domin tattaunawa da ƴan bindiga, ya yi kira da abi hanyar da tsohon shugaban ƙasa, Umaru Musa Yar'adua ya bi ya magance tsagerun Neja-Delta, domin kawo ƙarshen ayyukan ƴan bindiga.

Kara karanta wannan

Dikko Radda: Gwamnan Katsina da ya ce ba zai yi sulhu da ƴan bindiga ba

Me Gumi ya nemi a yi wa ƴan bindiga?

Tsohon sojan ya yi nuni da cewa abu ɗaya tsagerun Neja-Delta da ƴan bindiga ke yi, tun da dukkaninsu suna karya tattalin arziƙin ƙasar nan.

A cewarsa yayin da tsagerun Neja-Delta suke lalata bututun man fetur da sace ƴan ƙasashen waje, ƴan bindiga suna hana manoma zuwa gonakinsu su yi noma.

Ya yi nuni da cewa idan aka tattauna da ƴan bindigan, tare da yi musu afuwa kamar yadda aka yi wa tsagerun Neja-Delta, matsalar za ta zo ƙarshe.

'Hukuncin da ya dace da Mamu' - Gumi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya yi magana kan zargin ɗaukar nauyin ta'addanci da ake yi wa Tukur Mamu.

Sheikh Gumi ya bayyana cewa idan har kotu ta same shi da laifi, ya kamata a yi masa hukuncin da ya dace da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel