Sheikh Gumi Ya Fadi Kuskuren da Gwamnati Ke Yi Wajen Ceto Daliban da Aka Sace a Kaduna

Sheikh Gumi Ya Fadi Kuskuren da Gwamnati Ke Yi Wajen Ceto Daliban da Aka Sace a Kaduna

  • Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya yi magana kan ɗaliban da ƴan bindiga suka yi awon gaba da su a jihar Kaduna
  • Malamin addinin musuluncin ya yi nuni da cewa amfani da ƙarfin tuwo kan ƴan bindigan ba zai haifar da ɗa mai ido ba
  • Ya shawarci gwamnati da ta samar da shirin yin afuwa ga ƴan bindiga domin kawo ƙarshen matsalar gaba ɗaya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Babban malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmed Abubakar Gumi, ya yi magana kan kuskuren da gwamnatin tarayya ke yi wajen ceto ɗalibai 287 da malamansu da aka sace a jihar Kaduna.

Sheikh Gumi ya nuna cewa kuskure ne amfani da ƙarfi wajen ganin an ceto ɗaliban a hannun ƴan bindiga.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun fadi makudan kudin da za a biya kafin su sako daliban da suka sace a Kaduna

Sheikh Gumi ya fadi kuskuren gwamnatin tarayya
Sheikh Gumi na son gwamnati ta daina amfani da karfi kan 'yan bindiga Hoto: @IU_Wakili
Asali: Twitter

Da yake magana a wani shirin gidan talabijin na Arise tv, a ranar Alhamis a Abuja, Gumi ya ce ya kamata gwamnati ta matsa kusa da ƴan bindigan ta yi nazari a kansu domin samar musu da ingantacciyar rayuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Ahmed Gumi ya faɗi kuskuren gwamnati

A cewarsa, amfani da ƙarfi da gwamnati ke yi yanzu ya mayar da ƴan bindigan sun zama dodanni.

A kalamansa:

"Waɗannan ƴan bindigan suna ƙara ta’azzara. A baya basu yin haka. Ƴan ƙananan marasa rauni suke farmaka, ƙara ƙarfinsu za mu danganta shi da ƙarfin da ake amfani da shi a kansu.
"Yanzu muna yaƙar ƴan bindiga. Ba a san sunansu ba. Ba za a iya faɗa da wanda ba a sani ba. Mun ce a shiga, a gano su, mu tsara su, mu san su waye da kuma inda suke.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi kudin fansan da gwamnatinsa za ta biya don ceto daliban da aka sace a Kaduna

"Duk waɗannan bayanan sirri kusan babu su. Hanyar amfani da ƙarfin da ake bi ita ce ke ƙara tarɓarɓar da lamarin.
"Yanzu haka suna garkuwa da yara tare da barazanar kisa, wanda a da ba su yi ba. Don haka, ina tunani abin da ya kamata shi ne a koma a sake lale a daina amfani da ƙarfi.

Wace za a kawo ƙarshen ƴan bindiga?

Akan yadda za a kawo ƙarshen matsalar, ya ce kamata ya yi gwamnati ta tsara wani shiri kamar irin shirin yin afuwa ga tsagerun Neja-Delta da aka yi a baya.

A kalamansa:

"Ana buƙatar shiri kamar na Neja-Delta, shirin da zai fitar da su daga dazuzzuka, ilimantar da su, ba su kiwon lafiya, ba su ingantacciyar rayuwa.
"A haka ake sanya wa mutane su bar tashin hankali da fitina. Amma idan aka ci gaba da jefa bama-bamai, ba za su ji tausayin yaranmu ba. Kayi min inyi maka ne. Abin da ke faruwa kenan. Don haka ya kamata mu canja tsari, mu canja hanyar da muke bi."

Kara karanta wannan

Fasinjoji da dama sun bace yayin da 'yan bindiga suka farmaki wata mota a Taraba

An gargaɗi Tinubu kan Sheikh Gumi

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban fasto a Najeriya, Primate Elijah Ayodele, ya gargaɗi gwamnatin tarayya kan ba Sheikh Ahmed Gumi, damar jagorantar sulhu da ƴan bindiga.

Fasto Ayodele ya yi nuni da cewa bai kamata farar hula ya jagoranci sulhu da ƴan bindiga ba, sai dai idan dama ya kasance ɗaya daga cikinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel