Babban Coci a Najeriya Ya Karrama Sheikh Gumi Kan Dalili 1 Tak, Malamin Ya Sha Mamaki

Babban Coci a Najeriya Ya Karrama Sheikh Gumi Kan Dalili 1 Tak, Malamin Ya Sha Mamaki

  • Sheikh Ahmad Gumi ya samu gagarumar kyauta ta karramawa daga wani babban coci a jihar Kaduna saboda gudunmawar zaman lafiya
  • Gumi ya karbi kyautar ce da Fasto Christoper Solomon a matsayin malaman addinin da su ke kokarin kawo zaman lafiya
  • Cocin Cherubim da Seraphim a jihar Kaduna ya karrama malaman a matsayin ‘Jakadun zaman lafiya’ a jihar da kasa baki daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna – Cocin Cherubim da Seraphim a jihar Kaduna ya karrama Sheikh Ahmad Gumi kan inganta zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Har ila yau, cocin ya karrama Fasto Yohanna Buru wurin tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’umma.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya sun fusata yayin da shugaba Tinubu ya umarci gwamnan PDP ya canza kasafin 2024

Sheikh Gumi ya samu karramawa daga babban coci a Najeriya
Babban Coci a Najeriya ya karrama Gumi da wani Fasto kan zaman lafiya. Hoto: Christianity.com, Sheikh Ahmad Gumi.
Asali: Facebook

Mene dalilin karrama Gumi da Fasto?

Kamar yadda Fasto Christopher Solomon ya tabbatar, sun zabi Gumi da Buru ne don gudunmawar da su ke bayarwa a zaman lafiyar al’umma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce mutanen biyu an karramasu da ‘Jakadun zaman lafiya’ saboda himmatuwarsu a kokarin inganta zaman lafiya, cewar Tribune.

Ya ce:

“Kokarinsu na kawo zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’umma musamman tsakanin addinai shi ne dalilin karrama su.
“Sun yi kokari wurin tabbatar da rage tsattsauran ra’ayin addini da kuma cece-kuce a tsakanin mabiya addinai daban-daban.”

Wane martani Gumi da Faston su ka yi?

Yayin martaninsu bayan karbar kyautar, Gumi da Buru sun nuna jin dadinsu tare da yi wa ubangiji godiya kan wannan karramawa.

Sun kuma kirayi sauran Musulmai da Kiristoci da su zauna lafiya da junansu ba tare da wani bambanci ba a tsakani.

Kara karanta wannan

APC ta yi nasara yayin da kotu ta dakatar da INEC kan sake zaben 'yan Majalisu 27, ta tura gargadi

Malaman addinan sun kuma bukaci Gwamnatin Tarayya da ta kawo karshen rashin tsaro da ya yi katutu a fadin kasar baki daya.

Daga karshe, sun yi addu’ar neman zaman lafiya da fahimtar juna a jihar Kaduna da ma daukacin kasar baki daya, cewar Abatimedia.

Gumi ya bude asusun taimakon Falasdinawa

A wani labarin, Sheikh Amhad Gumi ya bude asusun taimakawa Falasdinawa yayin da ake ci gaba da gwabza yaki tsakaninsu da Isra’ila.

Gumi ya bayyana haka ne yayin wani karatu da ya ke gabatarwa a Masallacin Sultan Bello da ke birnin Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel