Jami’an Tsaro Sun San Maboyar ’Yan Bindiga, Sheikh Gumi Ya Magantu Kan Afuwa Ga Miyagu

Jami’an Tsaro Sun San Maboyar ’Yan Bindiga, Sheikh Gumi Ya Magantu Kan Afuwa Ga Miyagu

  • Fitaccen malamin addini a Najeriya, Sheikh Ahmed Gumi ya sake magana kan sulhu da ‘yan bindiga a Najeriya
  • Malamin ya ce jami’an tsaron kasar sun san inda maboyar ‘yan bindigar ta ke inda ya ce tare suke zuwa a baya
  • Sheikh Gumi ya fadi haka ne yayin hira a tashar rediyo a jiya Litinin 18 ga watan Maris inda ya bukaci a yi musu afuwa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna Sheikh Ahmed Gumi ya bayyana cewa jami’an tsaro sun san maboyar ‘yan bindiga a Arewacin Najeriya.

Ahmad Gumi ya ce lokacin da ya ke jagorantar sulhu duk da jami’an tsaro ya ke zuwa cikin daji domin yin magana da su.

Kara karanta wannan

Yadda za a bi a maido Dalar Amurka N160 daga N1600 Inji Masanin tattalin arziki

Gumi ya yi magana kan afuwa ga 'yan bindiga a Arewacin Najeriya
Sheikh Gumi ya bukaci sulhu da 'yan bindiga domin ceto dalibai a Kaduna. Hoto: Ahmed Gumi.
Asali: Facebook

Bukatar Gumi ga Tinubu kan 'yan bindiga

Shehin malamin ya bayyana haka ne a yammacin jiya Litinin 18 ga watan Maris yayin hira da gidan rediyon Nigeria Info FM.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya ce har yanzu ya na kan bakarsa na a tattauna da ‘yan bindigan da suka sace dalibai 287 a makarantar Kuriga.

Ya ce wannan ita ce hanya daya kacal da za a tabbatar da dawowar daliban ba tare da samun matsala ba, cewar BusinessDay.

“Ban yi tsammanin jami’an tsaron na fada muku gaskiya ba, lokacin da nake zuwa wurin ‘yan bindiga tare muke zuwa da su, ba ni kadai nake zuwa ba.”

- Ahmed Gumi

Gumi ya fadi halin da maharan ke ciki

Sheikh Gumi ya kara da cewa ya kamata Gwamnatin Tarayya ta sasanta da su inda ya ce sasantawar ba wai shi ne biyan kudi ba, sai dai a sakar musu ‘yan uwa da ke daure.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun faɗi malamin Musulunci 1 da suke goyon bayan ya tattauna da ƴan bindiga

Ya ce mafi yawan ‘yan bindigan an ware su babu makarantu da ruwan sha da hanyoyi masu kyau da sauran abubuwan more rayuwa, cewar TVC News.

Ya kuma bukaci Gwamnatin Tarayya ta yi musu afuwa kamar yadda ta yi a yankin Neja Delta domin dakile tsaro a Arewacin Najeriya.

Gumi ya kuma bayyana kalar ‘yan bindigar da cewa mafi yawansu makiyaya ne ‘yan Najeriya sai wasu ‘yan kasashen ketare kadan.

Gumi ya shirya jagorantar sulhu da mahara

Kun ji cewa Sheikh Ahmed Gumi ya shawarci Gwamnatin Tarayya kan sulhu da ‘yan bindiga a Arewacin Najeriya.

Gumi ya ce a shirye ya ke a kowane lokaci domin jagorantar sulhu da maharan idan Gwamnatin Tarayya ta bukaci hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel