Albashin ma'aikatan najeriya
Dangane da karin albashi, kungiyar 'yan fansho ta NUP ta koka kan cewa har yanzu akwai tsofaffin ma'aikata da ake biya N1,500 a wata matsayin kudin fansho.
Bayan janye tallafin man fetur wanda ya haifar da tsadar rayuwa a Najeriya, akwai gwamnonin jihohi 12 da suka yi karin albashi. Legas da Ondo na biyan N35,000.
A tsawon lokacin watan Ramadan, ma’aikatan gwamnati a jihar Zamfara za su je ofis da karfe 9 na safe kuma su tashi da karfe 3 na rana tsakanin Litinin da Alhamis.
Sakamakon rashin albashi mai tsoka da alawus-alawus da kuma karin girma, likitoci 59 da ke aiki a asibitin kwararru na Dalhatu Araf (DASH), Nasarawa sun ajiye aiki.
Yayin da aka shiga azumin watan Ramadana, Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sokoto ya amince da biyan rabin albashin ma'aikata domin gudanar da azumin cikin walwala.
Sanata Shehu Sani ya nuna shakku kan ko gwamnati =n Najeriya za ta iya aiwatar da mafi karancin albashi na N794,000 da kungiyar kwadago ta kasa ta nema.
Kungiyar kwadago ta Najeriya da takwararta ta TUC a jihar Akwa Ibom sun bukaci N850,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma’aikata a jihar.
Kungiyoyin NLC da TUC a matakin jihohi na ci gaba da bayyana sabon mafi ƙarancin albashin da suke buƙata daga gwamnati duba da matsin rayuwar da ake ciki.
Kungiyar Kwadago ta NLC ya bukaci karin mafi karancin albashi dubu 794 ga ma'aikatan yankin Kudu maso Yamma yayin da ake cikin matsin tattalin arziki.
Albashin ma'aikatan najeriya
Samu kari