Ma’aikatan Lantarki Sun Juyawa Gwamnati Baya, Sun Bukaci a Janye Karin Kudin Wuta

Ma’aikatan Lantarki Sun Juyawa Gwamnati Baya, Sun Bukaci a Janye Karin Kudin Wuta

  • Kungiyar da ke kula da ma’aikatan wutar lantarki ta soki matakin da aka dauka na tashin kudin shan wuta a Najeriya
  • ‘Yan sahun farko za su rika kashe N225 wajen sayen kowane KwH na lantarki, NUEE ta ce hakan ba zai taimaki kasar ba
  • Tsoron da Sakataren kungiyar NUEE yake yi shi ne barazanar da aka jefa ma’aikatansu da ke zuwa karbar kudin wuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Kungiyar NUEE ta ma’aikatan wutar lantarki ta bukaci gwamnatin tarayya ta janye karin kudin da aka yi wa wasu a kasar nan.

Karin kudin wutan bai samu karbuwa daga mafi yawan al’umma ba, kungiyoyin kwadago har da ‘yan majalisu sun soki tsarin.

Kara karanta wannan

Fusatattun Yarbawa na son a raba Najeriya, sun farmaki sakateriyar gwamnati a Oyo

wutar lantarki
Ma’aikata sun soki tashin kudin wutar lantarki a Najeriya Hoto: Getty Images/Sirisak Boakaew
Asali: Getty Images

Karin kudin lantarki ana cikin kunci

Daily Trust ta rahoto NUEE ta na cewa karin kudi a daidai lokacin nan da abubuwa suka yi wahala zai jawo karin tsada rayuwa ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakatare Janar na kungiyar, Dominic Igwebike ya aika wasika zuwa ga Ministan makamashi, ya ba da shawarar a janye karin.

Hadarin karin kudin lantarki

Igwebike ya ce karin kudin wutan zai jawo mutane su koma amfani da kayayyakin kasashen waje domin na gida sun tashi sosai.

A karshe dai kungiyar ma’aikata wutar lantarkin ta ce za a kashe kasuwancin gida.

NUEE ta yi ikirarin karin kudin shan wutan bai da amfani da Najeriya, sannan za a jefa ma’aikatan lantarki a mummunan barazana.

Wasikar Igwebike ta shaidawa gwamnati abokan hulda za su aukawa ma’aikatansu lokacin da suka bukaci karbar kudin wuta.

Kara karanta wannan

Watanni 2 da maganar komawa APC, Abba ya dauko binciken Ganduje da iyalinsa

Ma'aikatan lantarki za su yajin-aiki?

Kafin nan Punch ta rahoto ma’aikatan suna batun shiga yajin aiki saboda yadda aka tashi kudin duk KwH zuwa N225 ga ‘yan sahun farko.

Shugaban NUEE ya soki tsarin da aka fito da shi, ya ce an ware dinbin mutanen da suka dogara da lantarki wajen ayyukan yau da gobe.

Adebiyi Adeyeye ya ce har kasashen da aka cigaba suna biyan tallafin wutar lantarki.

Atiku ya soki tashin kudin lantarki

Ana da labarin yadda karin kudin wutar lantarki ya jawo Atiku Abubakar ya dauki zafi a kan Gwamnatin Bola Tinubu da ke mulki.

Wazirin Adamawa ya koka da tashin farashin dizil, karin ruwa a bashin banki da tashin albashi, ya ba da muhimman shawarwari

Asali: Legit.ng

Online view pixel