Imam Odankaru: Gwamnati Ta Bar Tsohon Malamin Makaranta a Kuncin Rayuwa Bayan Ritaya

Imam Odankaru: Gwamnati Ta Bar Tsohon Malamin Makaranta a Kuncin Rayuwa Bayan Ritaya

  • Imam Odankaru Musa ya yi shekaru sama da 30 yana aikin gwamnati, a yau ya yi ritaya ba tare da ya taba hakkokinsa
  • Wannan dattijo ya yi koyarwa a makarantu kuma ya rike mukami a gwamnatin jihar Kogi tsakanin 1976 har zuwa 2017
  • Da farko malaman makaranta suna cabawa, amma a yau an bar Odankaru Musa babu hali kuma babu cikakkiyar lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kogi - Imam Odankaru Musa tsohon malami ne wanda ya karar da kuruciyarsa wajen koyar da dalibai, a yau yana cikin wahalar rayuwa.

Malam Imam Odankaru Musa ya yi amfani da shafin Facebook ya ba da labarin yadda ya samu kan sa a sanadiyyar rashin kulawar gwamnati.

Kara karanta wannan

NERC ta tsokano ‘yan kwadago, ana yi wa Tinubu barazana saboda kudin lantarki

Imam Odankaru Musa
Malam Imam Odankaru Musa yana neman taimako Hoto: Imam Odankaru
Asali: Facebook

Rayuwar Imam Odankaru Musa da zama malami

A shekarar 1976 aka dauki Imam Odankaru Musa a matsayin karamin malami, a lokacin ana ganin kimar malamai, ana biyan N60 a wata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan mutum yana da shaidar Grade II, yana karbar N120 a kowane wata. Wannan ya sa malamin ya nemi karin ilmi, har ya kammala a 1982.

A cewarsa, ganin yadda yake facaka sai iyayensa suka matsa masa ya yi aure. Sai dai abin takaicin shi ne a yau malamin nan abin tausayi ne.

Abubuwa sun tabarbarewa malaman makaranta

Sannu a hankali abubuwa suka tabarbare, aka daina biyan malamai albashi a kan kari, kudin nasu ya zama bai isa saboda tsadar rayuwa.

Imam Odankaru Musa ya ce ganin haka ya fara koyon ayyukan hannu domin ya iye rike iyalinsa da kyau; ya koyi kamar zane, dab’i da rini.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC zai ɗauki sababbin ma'aikata sama da 5,000 a jiharsa, ya faɗi dalili

Malamin ya ce a masallatai ya rika kwana a garuruwan Legas, Ibadan, Fatakwal Aba, Ikare, Akure, Onitsha da Kabba wajen neman na-kai.

Yayin da kabilun Igala suke mulki a jihar Kogi, Imam Odankaru da ire-irensu suka kara tagayyara, gwamnati tayi watsi da lamarin malamai.

Baya ga kabilanci a mulki, malamin ya ce an daina biyansu alawus da hakkoki, biyan giratuti ya zama tarihi, karin girma ya zama a takarda.

Malaman makaranta a gwamnatin Yahaya Bello

A shekarar 2019 Yahaya Bello ya zama gwamna kamar yadda Imam ya dade yana rokon Allah SWT, wannan bai share masa hawaye ba.

Zuwan Gwamna Yahaya Bello sai da malamai suka shafe watanni 19 babu albashi da sunan tantance ma’aikata, mutane suka shiga matsi.

Har yanzu dai Ebira ke mulki a jihar Kogi, Imam ya yi ritaya daga aiki tun 2017, ba a fara biyansa fansho ba sai a 2018, babu batun giratutinsa.

Kara karanta wannan

Ayyukan da Annabi Muhammad ke yawaita yi a kwanaki 10 na karshen Ramadan

Kamar yadda ya fada a Facebook, yana fama da rashin lafiya amma babu kudin asibiti, saboda haka mutane suke taimaka masa da kudi.

Giratutin tsohon ma’aikacin N8m ne amma da alama gwamnatin Kogi ba ta maganarsu.

Gwamnati ta gano zaluncin AEDC

Ana da labarin wani zalunci da kamfanin AEDC ya yi, ya rika saidawa kowa wutar lantarki a kan sabon farashin da aka yankewa wasu tsiraru.

Da aka gano haka, NERC ta ce dole DisCon zai biya tarar kudi Naira miliyan 200 kuma kamfanin raba wutan lantarkin zai maidawa mutane kudinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel