Hukumar Sojin Najeriya
Rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana cewa wani jirgin atisaye ya gamu da karamin hatsari a jihar Kaduna yayin komawa filin jirgin sojoji da karfe 2:55 na rana.
Wasu ƴan ta'adda da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ke sun farmaki garin da ake sake ginawa ƴan gudun jira a karamar hukumar Dikwa ta jihar Borno.
Ministan tsaron Najeriya, Muhammad Badaru, ya bayyana irin yadda rundunar sojojin Najeriya ke ci gaba da samun galaba kan masu tada ƙayar baya a faɗin kasar nan.
Sojojin rundunar Operation Hadarin Daji sun yi nasarar ceto mutane 15 daga hannun ƴan bindiga a kauyen Tsohuwar Tasha, ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda.
Rundunar sojin Najeriya ta yi magana kan jita-jitar juyin mulki inda ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da kokari wurin kare martabar dimukradiyya a kasar.
Yan bindiga sun sake tare titin zuwa garin Maradun, hedkwatar ƙaramar hukumar Maradum a jihar Zamfara, sun yi ajalin babban jigon PDP tare da wasu bayin Allah.
Miyagun ƴan bindiga sun kai sabbin hare-hare kauyukan kananan hukumomi biyu a jihar Benuwai a karshen makon nan, sun kashe soja da wasu mutane da dama.
Gwamnatin jihar Borno ta ce zuwa yanzun manyan shugabannin kungiyar Boko Haram da suka kagoranci kafa ta a 2009 sun mutu ko sun miƙa wuya ga hukumomi.
Jami’an tsaro a jihar Zamfara sun yi nasarar cafke wani kasurgumin dan ta’adda da ya addabi al’ummar jihar da hare-hare wanda suka sace daliban Jami'ar Gusau.
Hukumar Sojin Najeriya
Samu kari