Daga Karshe, Wasu Mutanen Zamfara Sun Tsira Daga Sharrin Bello Turji

Daga Karshe, Wasu Mutanen Zamfara Sun Tsira Daga Sharrin Bello Turji

  • Daga karshe hankulan mazauna kauyen Gidan Goga a karamar hukumar Maradun, jihar Zamfara ya kwanta bayan sun biya haraji
  • Kasurgumin ɗan bindigan nan, Bello Turji, ya kakaba musu Musu Harajin miliyan N20m kafin ranar Asabar ko su sha azabarsa
  • Bayanai daga wata majiya sun nuna cewa mutanen da suka gudu daga garin sun fara koma wa bayan jin labarin an biya kuɗin

Zamfara - Mazauna ƙauyen Gidan Goga a yankin ƙaramar hukumar Maradun, jihar Zamfara sun samu nasarar biyan harashin miliyan N20m da hatsabibin ɗan bindigan nan Bello Turji ya ƙaƙaba musu.

Punch ta tattaro cewa Turji ya rataya harajin miliyan N20m kan mazauna ƙauyen idan suna son zaman lafiya kuma ya umarci su biya kuɗin kafin ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba ko su fuskanci fushinsa.

Matsalar yan fashin daji a Zamfara.
Daga Karshe, Wasu Mutanen Zamfara Sun Tsira Daga Sharrin Bello Turji Hoto: punchng
Asali: Twitter

Wani haifaffen ƙauyen wanda ya roki a sakaya bayanansa saboda halin tsaro ya shaida wa jaridar cewa sun samu ikon biyan kuɗin jiya (ranar Lahadi).

Ya ƙara da cewa mazauna ƙauyen da suka yi gudun Hijira zuwa wasu wuraren sun fara komawa gidanjensu bayan samun labarin, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Mutane da yawa harda ni kaina mun koma kauyen mu saboda jin an biya kuɗin Harajin," inji Mutumin.

Mutumin ya jaddada cewa ƙauyen ya ƙara biyan wasu miliyan shida ƙari kan kuɗin harajin domin kubutar da wasu mutum Shida da mayaƙan Bello Turji suka sace makonnin da suka shige.

"Mun biya karin miliyan shida domin a sako wasu mutane shida da 'yan ta'adda watau yaran Bello Turji suka yi garkuwa da su."

Duk wani yunkuri na jin ta bakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda reshen jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu, ya ci tura domin wayarsa a kashe har zuwa lokacin da muke kawo muku wannan rahoton.

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Matashin Malami a Jihar Kwara, Sun Nemi Fansa

A wani labarin kuma Miyagun 'yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun sace Malamin Addinin Islama, ɗan uwansa da ɗansa a Kwara

Mahaifin waɗanda aka sace wanda sanannen limami ne yankin Ilorin, ya roki gwamnati da mutane masu fatan Alkairi su agaza masa wajen ceto su.

Ya bayyana cewa masu garkuwan sun kira sun nemi kudin fansa amma basu da halin biya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel