Hukumar Sojin Najeriya
Wasu sojojin Najeriya sun rasa rayukansu a jihar Delta bayan an yi musu wani mummunan kwanton bauna. Hedikwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta tabbatar da faruwar lamarin.
Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya bukaci hadin kan hukumar EFCC wurin dakile masu daukar nauyin ta'addanci domin kawo karshen matsalar.
Akalla mutane bakwai da suka hada da jarirai biyu da mata biyar ne dakarun sojoji na rundunar Hadarin Daji suka kubutar a yayin wani samame da suka kai dajin Zamfara
Miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki kan mutane a wata kasuwa a jihar Filato, sun halaka mutane bakwai yayin da wasu da dama suka ji raunuka ranar Lahadi.
Jami'an rundunar sojin Najeriya sun yi nasarar murƙushe ɗaruruwan yan ta'adda a sassa daban-daban na ƙasar nan, sun kamo wasu sama da 100, sun ceto mutum 46.
Wasu yan bindiga sun kai hari kauyen Mbaikyor Mbalom da ke ƙaramar hukumar Gwer a jihar Benuwai, sun kashe rayukan mutane 17 da daren ranar Alhamis.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya bayyana cewa har yanzun ba a kamo hanyar da ta dace ba a kokarin kawo ƙarshen matsalar tsaro da talauci a Najeriya.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa dakarun sojoji sun shirya tunkarar kowace irin barazana idan bukatar hakan ta taso musamman a watan Ramadan.
Rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana cewa wani jirgin atisaye ya gamu da karamin hatsari a jihar Kaduna yayin komawa filin jirgin sojoji da karfe 2:55 na rana.
Hukumar Sojin Najeriya
Samu kari