Hukumar Sojin Najeriya
Gwamnatin jihar Borno ta ce zuwa yanzun manyan shugabannin kungiyar Boko Haram da suka kagoranci kafa ta a 2009 sun mutu ko sun miƙa wuya ga hukumomi.
Jami’an tsaro a jihar Zamfara sun yi nasarar cafke wani kasurgumin dan ta’adda da ya addabi al’ummar jihar da hare-hare wanda suka sace daliban Jami'ar Gusau.
Harbe-harben sojoji ya yi ajalin mutuwar mutane biyu da jikkata wasu mutane a jihar Delta yayin da ‘yan Najeriya ke fama da hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa.
Dattawan jihar Ekiti sun yi Allah wadai da masu kira ga sojoju su yi wa gwamnati mai ci juyin mulki kan halin matsin tattalin arziki da taɓarɓarewar tsaro a ƙasa.
Rundunar sojin Operation Safe Haven da haɗin guiwa jami'an wasu hukumomin tsaro sun sheƙe ƴan bindiga 13 tare da kamo wasu da ake zargi sama da 20 a Filato.
Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa jami'anta sun ƙara nakasa ƙungiyar Boko Haram/ISWAP a wani samame da suka kai, sun kashe mayaka akalla 3.
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya yi kira ga rundunaar sojojiin Najeriya ta kara zage damtse a yaƙin da take da ƴan ta'adda da yan bindiga a Arewa ta Gabas
Mazauna kauyen Wurna a ƙaramar hukumar Kurfi ta jihar Katsina sun fantsama zanga-zangar nuna adawa da yadda ƴan bindiga ke yawan kai musu hari ba ɗaga kafa.
Rundunar sojin Najeriya ta gargadi Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho kan irin kalaman da ya ke yi tun bayan dawowa Najeriya a ranar 22 ga watan Faburairu.
Hukumar Sojin Najeriya
Samu kari