Jirgin Rundunar Sojin Saman Najeriya Ya Gamu da Hatsari a Kaduna, Bayanai Sun Fito

Jirgin Rundunar Sojin Saman Najeriya Ya Gamu da Hatsari a Kaduna, Bayanai Sun Fito

  • Wani jirgin atisaye 'Super Mushshak' na rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) ya gamu da hatsari ranar Alhamis, 7 ga watan Maris, 2024
  • Mai magana da yawun NAF, AVM Edward Gabkwet, ya ce matukan da ke cikin jirgin, waɗanda ke dawowa daga ɗaukar horo, sun tsira daga hatsarin
  • Shugaban NAF, Air Marshal Hasan Abubakar, ya ba da umarnin a gudanar da bincike mai zurfi domin gano ainihin abinda ya haddasa haɗarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Wani jirgin ɗaukar horo na rundunar sojin saman Najeriya ya gamu da ɗan ƙaramin hatsari da misalin karfe 2:55 na ranar yau Alhamis a Kaduna.

Jirgin saman NAF ya yi karamin haɗari.
Mutum 2 sun tsallake yayin da jirgin rundunar NAF ya gamu da hadari a Kaduna Hoto: leadership.com
Asali: UGC

Daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin sama NAF, AVM Edward Gabkwet ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 7 ga watan Maris, 2024.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi ruwan wuta a sansanin ƴan bindiga a jihohin Arewa, sun kashe da yawa

Gabkwet ya ce lamarin ya faru ne a wuri mai nisan kilomita 3.5 daga filin jirgin saman soji na Kaduna, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane hali matukan jirgin suke ciki?

Ya ce haɗarin ya rutsa da matukan jirgin, waɗanda ke hanyar dawowa daga atisayen da suke fita da jirgin kamar yadda aka saba.

Kakakin sojin saman ya kuma ƙara da cewa dukkan matuƙan jirgin sun tsira lafiya ba tare da wani abu ya same su ba.

“Hatsarin wanda ya afku a kimanin mil 3.5 daga filin jirgin saman soji na Kaduna, ya rutsa da matukan jirgi 2 da ke dawowa daga atisayen da suka saba fita.
Bisa sa’a, matukan jirgin biyu sun fito daga jirgin lami lafiya."

- AVM Edward Gabkwet.

A ruwayar Channels tv, hafsan rundunar sojin sama, Air Marshal Hasan Abubakar, ya bada umarnin gudanar da bincike na farko kan hatsarin domin gano abinda ya jawo haɗarin.

Kara karanta wannan

Kano: Jerin albishir 5 da Gwamna Abba ya yi wa Sheikh Daurawa da Hisbah a zaman sulhu

Dakarun NAF sun yi luguden wuta a jihohi 2

A wani rahoton kuma jirgin rundunar sojin sama ya halaka ƴan bindiga masu yawa yayin da ya kai samame maɓoyar manyan ƴan ta'adda biyu a Zamfara da Katsina.

Mai magana da yawun NAF, AVM Edward Gabkwet, ya ce sojojin sun samu nasarori a farmakin da suka kai ranakun Talata da Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel