Gwamna Ya Fallasa Gaskiya, Ya Faɗi Kuskuren da Ake Tafkawa Kan Matsalar Tsaro da Talauci

Gwamna Ya Fallasa Gaskiya, Ya Faɗi Kuskuren da Ake Tafkawa Kan Matsalar Tsaro da Talauci

  • Malam Uba Sani ya bayyana cewa hanyoyin da ake bi da nufin magance talauci da matsalar tsaro a Najeriya kuskure ne
  • Gwamnan ya ce waɗannan kalubalen biyu sun zama alaƙaƙai da ke damun shugabannin siyasa a halin yanzu
  • Ya ce lokaci ya yi da masu ruwa da tsaki zasu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin tunkarar waɗannan matsaloli kuma su ga bayansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna, ya ce talauci da rashin tsaro sune manyan kalubalen da ke fuskantar Najeriya a halin yanzu.

Uba Sani ya ce shugabanni siyasa a ƙasar sun biyo hanyar da ba daidai ba wajen kawo ƙarshen waɗannan manyan ƙalubalen guda biyu.

Kara karanta wannan

"Saura ƙiris ku ji daɗi" Shugaba Tinubu ya aika saƙo ga ƴan Najeriya, ya kaddamar da sabon shiri

Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna.
Hanyar da Muka Bi Domin Magance Yunwa da Rashin Tsaro Kuskure ne, Gwamna Sani Hoto: Senator Uba Sani
Asali: Facebook

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a wajen taron zaman lafiya tsakanin mabiya addinai karo na shida tare da hadin gwiwar gwamnatinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta rahoto cewa taken taron shi ne "magance talauci da rashin tsaro a Najeriya: Nauyin da ya rataya a wuyan kowa."

Matsaloli 2 da suka addabi Najeriya

Gwamna Sani, wanda shi ne shugaban taron ya bayyana cewa talauci da rashin tsaro sune manyan kalubalen da kasar nan ke fama da su.

Ya ce waɗannan matsalolin biyu sun zama ƙarfen kafa kuma babban abin damuwa ga shugabannin siyasa a ƙasar nan.

Uba Sani ya ce:

“Talauci da rashin tsaro sune manyan kalubalen da kasar mu ke fuskanta. Ƙaruwar talauci shine babban abin da ke damun shugabannin siyasar mu.
"Kawar da talauci na da matukar muhimmanci wajen maido da kwarin gwiwar mutane a dimokuradiyya.

Kara karanta wannan

Ana ba tsaro a kasa, Akpabio ya fito ya fadi ci gaban da Tinubu ya kawo a bangaren

"Har yanzu muna ta fafutukar ganin mun magance kalubalen da ya hana mu ci gaba, musamman a fannin samar da ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, noma da tsaro."

Ya ce lokaci ya yi da ya kamata dukkan masu ruwa da tsaki su hada karfi da karfe domin tunkarar kalubalen da nufin kawo ƙarshensu, rahoton Within Nigeria.

A cewar gwamnan, bincike da kwararan shaidu ne ya kamata su zama a matakin farko wajen tantance hanyoyin warware fatara da dawo da tsaro a ƙasar nan.

Matasa sun yi zanga-zanga a Edo

A wani rahoton kuma matasa maza da mata sun ɓalle da zanga-zanga a kan yunkurin majalisar dokoki na tsige mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu

Masu zanga-zangar sun gargaɗi PDP ta dakatar da shirin tsige Shaibu domin za su iya haɗa kan jama'a su juya mata baya a zaɓe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel