Labaran tattalin arzikin Najeriya
Tsohon hadimin shugaban ƙasa a gwamatin Muhammadu Buhari, Bashir Hamad Ahmad, ya faranta ran ƴan Najeriya yayin da ya rahoto farashin Dala ya karye.
Farashin wasu kayayyaki kamar shinkafa (50kg) ya ragu da kashi 5.26 zuwa N90,000/buhu, sukari ya fadi da kashi 5.88 zuwa N80,000/buhu sakamakon darajar Naira.
Hukumar EFCC ta bayyana bankado wasu kudaden da take zargin an sace su a zamanin Buhari, inda ta ce a halin yanzu ana ci gaba da bincike don tabatar da hakan.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya nuna kwarin guiwar cewa ƴan Najeriya za su kubuta daga kangin wahala da tsadar rayuwa daga nan zuwa Disamba.
Darajar Naira ta ƙaru a kasuwar bayan fage wanda ƴan canji ke juyawa a Najeriya, rahoto ya nuna ana ana musayar Naira da Dalar Amurka kan N1,150.
Idan aka yi rashin sa'a, man kasar nan za su iya yin kwantai a kasuwar duniya. Najeriya na shan wahalar samun kudi a kasuwar duniya. Kasashe sun rage sayen mai.
Zuwa karshen 2024, masana sun ce Dala za ta kara karyewa. Goldman Sachs Group Inc ya kara burin da yake da shi a kan Naira, ya yi hasashen Dala za ta sauka kasa.
Farashin cinikayya a Najeriya ya fi na Amurka sau hudu zuwa biyar.An samu hauhawar farashi a kasashen Afirka 14. Bankin Duniya ya fadi dalilan da ya sa haka
Wani dan Najeriya ya bayyana yadda ya siya kati mai tsada bayan da gwamnati ta kara farashin wutar lantarki a makon da ya gabata kan wasu dalilai.
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari