Cikin Masu Boye Dala Zai Tsure, An Yi Hasashen Naira Za Ta Cigaba da Tashi a 2024

Cikin Masu Boye Dala Zai Tsure, An Yi Hasashen Naira Za Ta Cigaba da Tashi a 2024

  • Naira ta dauki lokaci tana kara daraja a kasuwa bayan kimar kudin Najeriyan ya fadi sosai a kan Dalar kasar Amurka
  • Masu canjin kudi a kasuwannin bayan fage na BDC sun tabbatar da an canji Dala a kan kimanin N1, 150 a makon nan
  • Kamfanin Goldman Sachs Group ya kara burin da yake da shi ga Naira, ya yi hasashen Dala za ta kai kasa da N1, 000

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Lagos - A ranar Juma’ar nan aka ji Naira ta sake kara daraja a kasuwannin canji inda aka saida kowace Dalar Amurka a kan N1, 150.

‘Yan canji da ke kasuwanci a Legas sun saye Dala a kan N1, 110 sannan suka rika saidawa a kan N1, 150 da makon nan ya zo karshe.

Kara karanta wannan

NFF ta nada 'dan Arewa a matsayin sabon mai horar da tawagar Golden Eaglets ta Nijeriya

Naira Dala
Naira ta tashi, ana hasashen Dala za ta kara karyewa a Najeriya Hoto: Liubomyr Vorona/Getty Images
Asali: Getty Images

Naira ta tashi a kan Dala a BDC

The cable ta ce kudin Najeriyan ya kara daraja da 0.86% a kan Dala ‘yan awanni kadan bayan an yi bikin karamar sallah a duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu cinikin kudin kasashen waje a kasuwar bayan fage suna cin ribar kimanin N40.

Wani ‘dan kasuwa ya shaida cewa sun ga kimar Dalar Amurka ta na sauka a kan Naira kuma ba su san abin da ya jawo hakan ba.

Dala: Naira ta kara daraja a FMDQ

A kafar FMDQ, haka lamarin yake domin Naira ta tashi da 7.16% ko a ce ta kara daraja da N88.23 zuwa N1,142.38/$ a ranar Juma’a.

The Nation ta rahoto Goldman Sachs Group Inc yana hasashen Naira za ta tashi sosai.

Idan hasashen kamfanin Amurkan ya tabbata, sai an saye Dala a kan kasa da N1000 bayan kwanaki sai da ta kusa kai N2000.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun yi martani kan lafta masu haraji a wani titin jihar Legas da Calabar

Da farko masana sun ce $1 za ta dawo N1, 200 ne a karshen 2024, amma dabarun CBN sun jawo ana ganin Naira za ta fi kara kima.

Yunkurin CBN na karya Dala kan Naira

A ranar Litinin da ta gabata, an saida Dala ne a kan N1,230.61 bayan yunkurin da bankin CBN ya yi wa ‘yan kasuwar bayan fage (BDC).

Gwamnan bankin CBN yana cigaba da yin bakin kokarinsa na ganin an samu isasshen kudin kasashen wajen da ake bukata a kasuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel