Labaran tattalin arzikin Najeriya
Sanata Natasha Akpoti ta sayi tirelolin abinci kuma ta rabawa al'umma musamman mabukata a mazaɓarta Kogi ta Tsakiya domin rage masu radadin tsadar rayuwa.
Dala ta kuma karyewa a kasuwar canji, $1 ta koma N1, 280 a kasuwar canji. Ribar N20 ne ‘yan canjin suke samu idan sun saida kowace dala a kasuwar bayan fage.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya saka sunayen Aliko Dangote, Abdulsamad Rabiu da wasu 'yan kasuwa a kwamitin farfado da tattalin arzikin Najeriya.
Yan canji sun musanta rahoton cewa Dala ta karye har an fara sayar da ita a kan N1000 kan kowace Dala ɗaya a kasuwa, sun ce a yanzu dai ta dawo N1,300.
Adadin bashin da ake bin Najeriya ya karu daga N87.91trn ($114.35bn) a zango na uku na shekarar 2023 zuwa N97.34trn ($108.23bn) a zango na hudu na shekarar 2023.
Babban bankin Najeriya (CBN) ya fitar sanarwar sayar da dala ga ƴan canji kan farashin N1,251/$1, ya ba su umarnin farashin da zasu sayar da kwastomomi.
Laifuffukan da ake tuhumar Binance sun haɗa da ƙin biyan harajin VAT, ƙin bayar da bayanan kuɗaɗen shiga don karɓar haraji, ƙin biyan harajin ribar kamfani (CIT).
Rahoto ya bayyana yadda bashin da ake bin Najeriya ya karu idan aka kwatanta da wanda ake bin kasar a shekarar da ta gabata bayan da Tinubu ya karbi mulki.
Gwamnoni 16 daga cikin 36 sun marawa yunkurin kafa ƴan sandan jihohi baya da nufin kawo ƙarshen matsalar tsaron da taƙi ci ta ƙi cinyewa a ƙasar nan.
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari