Dala Ta Daina Tsoron Gwamnan CBN: Shehu Sani Ya Yi Tsokaci Bayan Naira Ta Sha Bugu a Hannun Dala

Dala Ta Daina Tsoron Gwamnan CBN: Shehu Sani Ya Yi Tsokaci Bayan Naira Ta Sha Bugu a Hannun Dala

  • Sanata Shehu Sani ya yi martani game da faduwar darajar Naira zuwa ₦1,140 kan kowacce dala a kasuwar bayan fage a shafin sada zumunta
  • A ranar Alhamis, 18 ga watan Afrilu, darajar Naira ta fadi daga ₦1,060 kan kowacce dala, zuwa ₦1,169.99 kan kowacce dala
  • Sakon Sani ya janyo cece-ku-ce daga mabiyansa, inda wasu ke sukar yadda gwamnati ke tafiyar da lamurran tattalin arzikin Najeriya tare da yin kira ga kawo karshen faduwar kudin

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Najeriya - Sanata Shehu Sani, tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, ya yi martani game da labarin faduwar Naira zuwa ₦1,140 kan kowacce a kasuwar hada-hadar bayan fage.

Kara karanta wannan

A karon farko cikin kwanaki, naira ta ci karo da matsala, ta tashi da 1.3% a kasuwa

Naira ta ragu zuwa Naira 1,140 kan kowacce dala a kasuwa daga N1,060 kowacce dala a ranar Alhamis 18 ga watan Afrilu, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa darajar Naira ta fadi a kasuwar canji ta Najeriya (NAFEM), zuwa N1,169.99 kan kowacce dala.

Shehu Sani ya tabo CBN kan faduwar Naira
Shehu Sani ya tabo CBN kan batun da ya shafi dala da Naira | Hoto: CBN, Shehu Sani
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, farashin canji a kasuwar NAFEM ya tashi zuwa N1,169.99 kan kowacce dala daga N1,154.98 a ranar Alhamis, wanda ke nuni da faduwar darajar Naira da 15.01.

Tazarar da aka samu a sauyin farashin dala da Naira

Kasuwar ta ga hauhawar farashin dala zuwa N1,236 da kuma kasa zuuwa N1,021 a kowacce dala wanda hakan ba da tazarar N215 a tsakani.

Adadin dalar da aka yi cinikayyarta a kasuwar ya ragu da 53.2% zuwa dala miliyan 86.86 daga dala miliyan 185.62 a ranar Alhamis.

Tazarar da ke tsakanin kasuwar dalar Amurka da NAFEM ta ragu zuwa N29.99 kan kowacce dala daga N94.08 a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Gwamnatin jihar Gombe ta dawo da dokar sharar wata-wata

Martanin Sanata Shehu Sani kan kitimurmurar Naira da dala

Da yake martini ga abin da ya faru na tashin darajar dala, Shehu Sani ya yi tsokaci mai kama da shagube ga gwamnan CBN.

Ya ce:

“Dala mai taurin kai ta daina jin tsoron Cardoso kuma.”

A kwanakin baya ne gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Yemi Cardoso ya sha yabon ‘yan kasa yayin da Naira ta samu a kanta bayan shan duka a hannun dalar Amurka.

Yadda darajar Naira ya yi kasa kwanan nan

A tun farko, darajar naira ta sake faduwa a ranar Juma'a 19 ga watan Afrilu a kasuwannin 'yan canji, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

A jiya ana siyar da dala kan N1,169 a kasuwanni idan aka kwatanta da ranar Alhamis 18 ga watan Afrilu kan N1,154.

Wannan ne karon da aka samu naira ta dan yi kasa tun da ta fara farfadowa daga bugun da take sha a hannun dala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel