Tinubu Zai Saka Najeriya Cikin Jerin Kasashen Duniya Masu Arziki Inji Kashim Shettima

Tinubu Zai Saka Najeriya Cikin Jerin Kasashen Duniya Masu Arziki Inji Kashim Shettima

  • Mataimakin shugaban kasan Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ya bada tabbacin cewa shugaba Bola Tinubu ya shirya wurin saka Najeriya cikin manyan ƙasashe duniya masu arziki.
  • Sanata Kashim Shettima ya yi jawabin ne yau a fadar shugaban kasa yayin da tawagar kungiyar masu zuba jari (CWEIC) ta kawo masa ziyara.
  • Ya kuma bawa tawagar tabbacin cewa Najeriya a karkashin Bola Tinubu a shirye ta ke wajen maraba da masu zuba jari daga ko ina a fadin duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, sanata Kashim Shettima, ya bada tabbacin cewa Najeriya zata zama gaba-gaba a harkar tattalin arzikin duniya karkashin mulkin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Remi Tinubu: Matar shugaban kasa ta kaddamar da shirin tallafawa matan Arewa

Sanata Kashim Shettima
Sanata Kashim Shettima ya ce Najeriya za ta karbi masu zuba jari hannu bibbiyu. Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

A cewarsa, ya bada tabbacin ne saboda yadda gwamnatin ta dukufa wajen samar da yanayin da zai bunkasa harkar zuba jari.

Sanata Kashim Shettima ya yi jawabin ne a yau Laraba lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar masu zuba jari a fadar shugaban kasa, cewar Channels Television

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kashim Shettima ya kuma ba kungiyar tabbacin cewa gwamnatinsu za ta yi amfani da matasan da Allah ya albarkaci kasar da su wajen gina kasa mai aminci da cigaban tattalin arziki.

Najeriya ta shirya karbar masu zuba jari

Mataimakin shugaban kasar ya bada tabbaci ga shugabannin kungiyar zuba jarin yana mai cewa shugaba Bola Tinubu dan kasuwa ne saboda haka zai bada himma a kan duk abun da ya shafi harakar kasuwanci.

Kuma ya basu tababcin cewa gwamnatin ba za ta nuna bambanci tsakanin baki da 'yan kasa ba wajen basu damar gudanar da kasuwanci cikin aminci.

Kara karanta wannan

Yayin da NEF ta yi da-na-sanin zaben Tinubu, shugabannin Fulani sun fadi matsayarsu

A yayin da yake magana a kan irin shirin da Najeriya take da shi a harkar haɓakar tattalin arziki, mataimakin shugaban kasar ya ce Najeriya ce ya kamata ta ja hankalin duk wani mai zuba jari a duniya.

Ya fadi haka ne saboda, a cewarsa, kasar ta dauki haramar zama ta gaba-gaba a harkar tattalin arziki kuma za ta shiga cikin jerin ƙasashen duniya masu cigaban a karkashin Tinubu, a cewar jaridar Vanguard

Tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa

Ya kuma bayyana hasashen da aka yi a kan cewa nan da shekarar 2075 Najeriya za ta zama kasa ta uku a tattalin arziki a duniya.

Saboda haka Najeriya ita ce jogarar ƙasashen Afrika kuma tana shirye domin yin harkar kasuwanci da masu zuba jari daga ko ina a fadin duniya.

Tinubu ya yi tanadi wa 'yan Najeriya

A wani rahoton kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ya yi kira ga 'yan Najeriya da su kwantar da hankulansu domin shugaba Bola Tinubu ya yi masu kyakkyawan tanadi.

Mataimakin shugaban kasan ya yi jawabin ne domin karfafa 'yan Najeriya a kan matsin tattalin arziki da suke fuskanta yana mai cewa hakurinsu ba zai tafi a banza ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel