Farashin Man Fetur Ya Ragu a Wasu Gidajen Mai Yayin da Dala Ta Ƙara Karyewa a Najeriya

Farashin Man Fetur Ya Ragu a Wasu Gidajen Mai Yayin da Dala Ta Ƙara Karyewa a Najeriya

  • Wasu daga cikin gidajen mai a Legas sun rage farashin litar man fetur yayin da Naira ke ƙara farfaɗowa kan Dala a kasuwar canji
  • Saukar farashin fetur ka iya rage tsadar kudin sufuri da kuma rage nauye-nauyen da suka yi wa magidanta yawa a faɗin ƙasar nan
  • A halin yanzun, kuɗin Najeriya ya ƙara daraja mafi girma kan Dalar Amurka a cikin tsawon watanni bakwai da suka gabata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Farashin man PMS wanda aka sani da fetur ya ragu daga N640 da N660 da ake sayarwa a ƴan makonnin da suka shige zuwa N620 kan kowace lita a wasu wurare a jihar Legas.

Wannan sauki da aka samu a farashin litar Fetur ba zai rasa nasaba da tashin darajar Naira kan Dalar Amurka da ake ta samu a ƴan kwanakin nan ba.

Kara karanta wannan

Ana harin fetur ya koma N500, ‘yan kasuwa sun ci buri da matatun Fatakwal da Dangote

Gidan mai.
Sauƙi na kara samuwa yayin da farashin fetur ya kara sauka a gidajen mai Hoto: Benson Ibeaubuchi
Asali: Getty Images

Yayin da Legit Hausa ta ziyarci wasu gidajen mai mallakin kamfanin mai na ƙasa (NNPCL) a Legas ta gano cewa farashin fetur ya sauka zuwa N580 kan kowace lita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da har kawo yanzu NNPCL bai sanar da ci gaban a hukumance ba amma raguwar farashin fetur alama ce ta samun sauƙi yayin da ake fama da tsadar rayuwa.

Yadda farashin fetur ya sauka

Da yake tsokaci kan lamarin, wani manajan gidan mai da ya rage lita zuwa N620 a Legas, Kunle Ademola, ya ce farashin da suke karɓo man ne ya sa suka rage daga N650 zuwa N620.

"Kwanaki kaɗan da suka wuce mun kulle gidan mai amma yanzu kaya sun iso. Duk da wasu gidajen mai da ke kusa da mu suna sayarwa a kan N650, mun rage na mu zuwa farashin da bai ka haka ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun buɗe wa mutane wuta, sun kashe bayin Allah sama da 20 a Kaduna

"Mun sauke farashin lita ne saboda mun karɓi sabon kaya kan farashin da bai kai wanda muka biya a baya ba," in ji manajan.

Farashin Naira da man fetur

A wata hira, tsohon shugaban kungiyar ƴan kasuwar mai (IPMAN), Chinedu Okoronkwo, ya yi bayanin alaƙar musayar kuɗin Najeriya da farashin man fetur.

Ya ce:

"Ƴan Najeriya sun san cewa an cire tallafi, don haka mun zo wani zamani da yanayin kasuwa ne ke juya farashin. Matukar Dala za ta kara tsada, farashin fetur zai ci gaba da ƙaruwa."
"Haka abin yake idan kuma Naira ce ta ƙara daraja, ma'ana fetur zai sauko kenan."

Daga farkon makon nan zuwa yau, Naira ta tashi a kasuwar musayar kuɗi inda ta kusa dawo kusan $1/N1000.

Fetur ya kara tsada a Katsina

Wakilin Legit Hausa ya ziyarci wasu gidajen mai a jihar Katsina domin gano ko farashin ya sauka kamar yadda Dala ta ƙara daraja a kasuwa.

Kara karanta wannan

"Allah kaɗai ke ba da mulki," Atiku ya mayar da martani kan zargin cin amana a taron NEC

A binciken da muka yi, farashin man fetur ya tashi daga N700-720 zuwa N740-760 a wasu gidajen mai a jihar Katsina.

Wani mai ba da mai da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida mana cewa fetur ya kara tsada ne saboda a ƴan kwanakin nan an fara ƙarancinsa a jihar.

"A ƴan kwanakin nan mai ya yi ƙaranci wasu gidajen man a kulle su ke, nan ma kana ganin yadda muke fama da layi. Ban san dalili ba amma dai an ce mu ƙara kuɗin zuwa N740," in ji shi.

Haka nan wani ɗan bunburutu, Sabitu Mai Fetur, ya ce babu wata alamar mai zai sauko domin suna shan wahala kafin su samu a yanzu.

WYayin da wakilin mu ya ziyarci wasu gidan mai, ya taras da wasu a kulle wasu kuma an haɗa dogon layi a ƙaramar hukumar Ɗanja ta jihar Katsina.

Tinubu ya kaddamar da tsarin zamani

Kara karanta wannan

'Bam' da ƴan ta'adda suka dasa ya halaka bayin Allah sama da 10 a Arewacin Najeriya

A wani rahoton Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da sabon tsarin aiki wanda zai rage asarar makudan kuɗin shiga a Najeriya duk shekara.

Shugaban ƙasar ya ce Najeriya za ta ceto $4bn a kowace shekara ta hanyar rage ayyukan ofis da toshe hanyoyin cin hanci da rashawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel