Hukumar yan sandan NAjeriya
Dakarun ƴan sandan Najeriya sun yi nasarar gano motar Hon. Justice Azuka, ɗan majalisar dokokin jihar Anambra da aka yi garkuwa da shi ana gobe kirismeti.
Gwamna Alia na jihar Benuwai ya ce duk mai hannu a mummunan harin da ya yi ajalin mutum 11 ba zai tsira ba, zai tabbatar doka ta yi aiki a kansa duk daren daɗewa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindiga sun hallaka Rabaran Tobias Chukwujekwu Okonkwo a jihar Anambra bayan mummunan harin da aka kai masa a jiya Alhamis.
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, Clement Adesuyi Haastrup ya zama sabon sarki a masarautar Ijesa a matsayin Owa-Obokun bayan kada kuri'a kan nadin.
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kai farmaki wata maboyar barayi da suka sace Keke Napep a Danbatta. An mika Keke Napep din ga mai ita bayan bincike.
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama wani gawurtaccen dan daba da ke kunna rikicin daba a unguwannin Kofar Mata da Zango. Kabiru Jamilu Awu ya amsa laifinsa
Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta fito ta yi magana kan harin da ake cewa 'yan fashi da makami sun kai wa tawagar ayarin motocin Gwamna Ahmadu Fintiri.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a wasu kauyukan jihar Benue. 'Yan bindigan sun kashe mutane tare da yin garkuwa da kananan yara.
An shiga tashin hankali a jihar Anambra yayin da wasu mahara ɗauke da makamai suka sace ɗan majalisar dokoki, Justice Azuka a hanyar komawa gida.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari