Manyan Labarai A Yau
Shugabar hukumar kasuwanci ta duniya (WTO), Ngozo Okonjo-Iweala ta tabbatar da mutuwar shugaban bankin Access, Herbert Wigwe wanda ya mutu a hatsarin jirgin sama.
A wani yunkuri na dakile hare-haren da 'yan bindiga ke kaiwa wasu garuruwa a jihar Filato, Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da kafa wani sansanin sojoji a jihar.
Wasu mata da matasa sun gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki a birnin Legas. An yi zanga-zanga a wasu jihohin.
Hukumar kula da kwallon wasan nahiyar Afirika (CAF) ta sanar da cewa dan kasar Mauritania, Dahane Beida, ne zai hura wasan karshe tsakanin Najeriya da Cote d'Ivoire.
Herbert Wigwe, shugaban bankin Access Holding, mutum ne da ba za a taba mantawa da shi ba a matsayin daya daga cikin ma’aikatan banki mafi shahara.
Shugaban kamfanin Access Holdings Plc, Herbert Wigwe, ya yi bankwana da duniya. Mun tattaro muku abin da ya kamata ku sani dangane da rayuwar marigayin.
A ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu ya kamata a daura auren mataimakin Bursar na jami'ar jihar Kwara, Ayuba Olaitan, wanda ya rasu yayin kallon wasan Najeriya.
Hukumar da ke karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci a jihar Kano ta kai samame rumbun ajiyar masu boye kayan abinci domin haifar da tsadar kaya a kasuwa.
Jones Arogbofa, Birgediya Janar mai ritaya a rundunar sojin Najeriya wanda ya yi aiki a matsayin shugaban ma’aikatan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya rasu.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari