Najeriya vs Cote d'Ivoire: Malamin da Ya Yi Hasashen Nasarar Tinubu, Ya Yi Magana Kan Osimhen

Najeriya vs Cote d'Ivoire: Malamin da Ya Yi Hasashen Nasarar Tinubu, Ya Yi Magana Kan Osimhen

  • An bayyana Victor Osimhen, ɗan wasan Super Eagles, a matsayin abin koyi saboda rawar da yake takawa a gasar AFCON 2023
  • Fasto Joshua Iginla, wanda a shekarar 2022 ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu ne zai lashe zaɓen 2023, ya yi wannan tsokaci inda ya ce Osimhen ba shi ne yake zura kwallo a raga ba amma ya fi shahara a ƙungiyar
  • Daga nan malamin addinin ya ƙara da cewa a rayuwa ba wai zama a gaba ba ne, sai dai zama a inda ya dace da yin abin da ya dace

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Fasto Joshua Iginla na Champions Royal Assembly in Abuja, ya yi tsokaci kan ɗan wasan Najeriya, Victor Osimhen, na Super Eagles.

Kara karanta wannan

Herbert Wigwe: Abubuwan sani 7 game da shugaban bankin Access da ya mutu a hatsarin jirgi

Fasto Iginla shi ne wanda ya yi hasashen nasarar Shugaba Bola Tinubu a 2022 kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Fasto Iginla ya yi magana kan Osimhen
Fasto Iginla ya fadi abun koyi dangane da Victor Osimhen Hoto: Super Eagles, Iginla Ministries
Asali: Twitter

A wata huɗuba da ya yi a wani faifan bidiyo a shafin YouTube na cocin da aka sanya a ranar Juma’a, 9 ga watan Fabrairu, malamin ya ce Osimhen ba shi ne ɗan wasan da ya ci wa Najeriya ƙwallo ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da haka, shi ne dan wasan da aka fi yin magana a kansa a cikin tawagar Super Eagles.

Fasto Iginla ya bayyana darasin da za a koya daga Osimhen

Daga nan sai fasto Iginla ya buƙaci mabiyansa da su riƙa yin aikinsu yadda ya kamata, inda ya ƙara da cewa ba wai zama a gaba ba ne a abu mafi muhimmanci, a’a sai dai yin abin da ya kamata.

Kara karanta wannan

AFCON: Fitaccen ɗan kasuwa ya mutu yana tsaka da kallon wasan Najeriya da Afirka ta Kudu

Iginla ya ce:

“Akwai wani dogo, matashi mai suna Osimhen, ba shi ne ke zura kwallo a raga ba, amma ya fi wanda ya zura kwallo farin jini saboda shi yana wasa ne don nasarar tawagar, kowane ne kuwa ya zura ƙwallon.
"A rayuwa idan ka taka rawarka yadda ya kamata, ba za a iya yi maka kallon na ɗaya ba, amma idan ka yi aikinka yadda ya dace, za a fi yin alfahari da kai."

An fitar da faifan bidiyon ne bayan da Super Eagles ta Najeriya ta doke Bafana Bafana ta Afirka ta Kudu a wasan da suka tashi 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan da kungiyoyin biyu suka buga 1-1 a wasan da aka saba yi a cikin mintuna 90 da ƙarin minti 30.

Malamin ya kuma yi wannan tsokaci ne a lokacin da ƴan wasan Najeriya ke shirin karawa da The Elephant na Cote d’Ivoire a wasan ƙarshe na gasar cin kofin AFCON 2023.

Kara karanta wannan

Babban malamin addini ya fallasa fastoci masu shirya mu'ujizar karya, ya fadi yadda suke yi

Ga bidiyon nan ƙasa:

Shugaba Tinubu Ya Fasa Halartar Wasan Karshe Na AFCON

A wani rahoton kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ba zai halarci kallon wasan ƙarshe na gasar AFCON 2023 ba a ƙasar Cote d'Ivoire tsakanin Najeriya da ƙasar mai masaukin baƙi.

A maimakon hakan, shugaban ƙasan ya tura mataimakinsa Kashim Shettima tare da wata tawaga domin nuna goyon baya ga Super Eagles.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel