Zanga-Zanga Kan Tsadar Rayuwa Ta Ci Gaba da Yaduwa a Sassan Najeriya, Bayanai Sun Fito

Zanga-Zanga Kan Tsadar Rayuwa Ta Ci Gaba da Yaduwa a Sassan Najeriya, Bayanai Sun Fito

  • Zanga-zanga kan tsadar rayuwa da ake yi a Najeriya ta isa birnin Legas domin nuna adawa kan farashin kayayyaki ya yi tashin gwauron zabi
  • Wasu mata da matasa ƴan kasuwa a yankin Ibeju-Lekki sun fito domin nuna adawa kan yadda rayuwa ke ci gaba da yin tsada
  • Masu zanga-zangar sun riƙe kwalaye masu rubucen da ke tunatar da shugaban ƙasa Bola Tinubu cewa akwai yunwa a ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Al’ummar Legas sun bi sahun jihohin da aka gudanar da zanga-zangar nuna rashin gamsuwa da tsadar rayuwa a ƙasar nan.

A Legas, mata da matasa ƴan kasuwa sun yi zanga-zanga a unguwar Ibeju-Lekki da ke jihar Legas a ranar Asabar, 10 ga watan Fabrairu, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta shiga sabuwar matsala kan tuhumar tsohon gwamna, bayanai sun fito

An yi zanga-zanga a Legas
An gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa a Legas Hoto: channelstv
Asali: Facebook

Sun ɗauki kwalaye masu rubuce-rubuce irin su “Baba Tinubu, ƴan Nijeriya suna jin yunwa” da ‘Tinubu, ka zo ka cece mu’ da dai sauransu, rahoton Vanguard ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga-zangar ita ce ta baya-bayan nan a jerin zanga-zangar da aka gudanar a jihohin Kogi da Osun da Neja da kuma Kano kan tsadar rayuwa a ƙasar nan.

Tun bayan cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023, farashin kayan masarufi ya yi tashin gwauron zabi a ƙasar nan.

Wannan tsadar kayayyakin tare da faɗuwar darajar Naira ya sanya an shiga halin matsi a cikin Najeriya, inda mutane ke kokawa kan yadda rayuwa ta yi matuƙar tsada.

Sabuwar zanga-zanga ta ɓarke kan tsadar rayuwa

Labari ya zo cewa biyo bayan zanga-zangar da aka yi a jihar Neja kan tsadar rayuwa, wata sabuwar zanga-zangar ta sake ɓarkewa a birnin Suleja, na jihar Neja..

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara kan 'yan ta'adda a jihar Katsina

Masu zanga-zangar dai sun fito kan tituna domin nuna adawarsu kan yadda rayuwa ta yi tsada a ƙasar nan.

Masu zanga-zangar sun yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya kawo karshen wannan tsadar rayuwa saboda suna cikin wahala.

Ƴan Sanda Sun Cafke Masu Zanga-Zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Neja ta cafke wasu mutum 25 kan jagorantar zanga-zanga a birnin na jihar Neja.

Rundunar ta tabbatar da cewa za ta tura su zuwa kotu da zarar kammala bincike kan tuhumar tayar da tarzoma a yayin zanga-zangar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel