Najeriya vs Cote d'Ivoire: CAF TA Fadi Alkalin Wasan da Zai Hura Wasan Karshe Na AFCON 2023

Najeriya vs Cote d'Ivoire: CAF TA Fadi Alkalin Wasan da Zai Hura Wasan Karshe Na AFCON 2023

  • Ɗan ƙasar Mauritaniya, Dhahane Beida ne zai hura wasan ƙarshe na AFCON 2023 tsakanin Najeriya da Cote d'Ivoire
  • Super Eagles ta Najeriya da The Elephants ta Cote d'Ivoire za su fafata a gasar cin kofin AFCON a filin wasa na Alassane Ouattara da ke Abidjan
  • Wasan ƙarshe na AFCON zai kasance karo na uku da alƙalin wasan mai shekara 32 zai hura a gasar TotalEnergies CAF AFCON ta bana

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Abidjan, Cote d'Ivoire - Dahane Beida mai shekara 32 ɗan ƙasar Mauritania ne zai hura wasan ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar Afirika (AFCON 2023), tsakanin Najeriya da Cote d'Ivoire.

Wasan tsakanin Super Eagles na Najeriya da The Elephants na Cote d'Ivoire zai gudana ne filin wasa na Alassane Outtara da ke birnkn Abidjan a ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

AFCPN 2023: Kocin Cote d'Ivoire ya fadi hanyar da za su bi don doke Najeriya a wasan karshe

Dahane Beida zai hura wasan karshe
CAF ta sanar da Dahane Beida a matsayin wanda zai hura wasan karshe na AFCON Hoto: CAF Online
Asali: UGC

Hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar Afrika (CAF) ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ta shafinta na yanar gizo, CAF Online a ranar Asabar, 10 ga watan Fabrairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasan ƙarshe da za a yi a filin wasa na Alassane Ouattara da ke Abidjan zai kasance karo na uku a da alƙalin wasan ya hura wasa a gasar TotalEnergies CAF AFCON ta bana.

Wasanni na wa Baida ya hura a AFCON 2023?

CAF ta ce Beida shi ne alƙalin wasa a wasan da aka buga tsakanin Masar da Mozambique a matakin rukuni da karawar zagaye na 16 tsakanin Angola da Namibia.

Beida zai samu taimakon ɗan ƙasar Angola, Emiliano Dos Santos, ƴar ƙasar Zambia, Diana Chicotesha, yayin da Bouchra Karboubi na ƙasar Morocco zai zama mataimakin alƙalin wasa na huɗu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu zai lula zuwa kallon wasan ƙarshe na gasar cin kofin Afirka AFCON? Gaskiya ta bayyana

Mataimakin alƙalin wasa na ɓangaren VAR zai kasance Mahmoud Ashour daga Masar, yayin da Rivet Maria Pakuita daga ƙasar Mauritius za ta zama matsayin mataimakiyar alƙalin wasa ɓangaren VAR.

Shugaba Tinubu Ba Zai Halarci Wasan Ƙarshe Na AFCON Ba

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ba zai halarci wasan ƙarshe na gasar cin AFCON ba tsakanin Najeriya da Cote d'Ivoire.

Shugaban ƙasar ya tura wata tawaga ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, domin nuna goyon baya ga tawagar Super Eagles.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel