Tsohon Shugaban Ma’aikatan Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Ya Kwanta Dama
- Tsohon shugaban ma'aikatan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Janar Jones Oladeinde Arogbofa (mai ritaya), ya kwanta dama
- Arogbofa, haifaffen garin Oka-Akoko, jihar Ondo, ya yi fice a aikin soja bayan da ya shiga aikin a shekarar 1973
- Arogbofa ya halarci makarantu daban-daban ciki harda jami'ar Obafemi Awolowo, ya kuma rike mukamin shugaba a cibiyar CRIMMD har zuwa lokacin mutuwarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Janar Jones Oladeinde Arogbofa (mai ritaya), tsohon shugaban ma'aikatan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kwanta dama.
Arogbofa, wanda ya kasance Birgediya Janar mai ritaya, ya mutu a safiyar ranar Asabar, 10 ga watan Fabraoru, yana da shekaru 72 a duniya, jaridar New Telegraph ta ruwaito.
Babu cikakken bayani kan abin da ya haddasa mutuwar tsohon jigon rundunar sojin, kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Takaitaccen tarihin Jones Oladeinde Arogbofa
An haifi Arogbofa a garin Oka-Akoko, jihar Ondo a ranar 10 ga watan Nuwamban 1952. Ya shiga aikin sojan Najeriya a shekarar 1973 kuma ya yi fice.
Arogbofa ya yi aiki a matsayin tsohon shugaban ma'aikatan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan tsakanin ranar 10 ga watan Fabrairun 2014, da Mayun 2015.
Makarantun da ya halarta sun hada da jami'ar Obafemi Awolowo, makarantar fasaha ta Rochester, Jami'ar Alabama, makarantar soji ta Amurka, jami'ar Legas da jami'ar Ibadan.
Har zuwa lokacin mutuwarsa, Arogbofa shine shugaban cibiyar bincike, kula da bayanai da ci gaban watsa labarai (CRIMMD).
Fitacciyar jarumar fim ta riga mu gidan gaskiya
A wani labarin, mun ji cewa fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Ethel Ekpe ta riga mu gidan gaskiya, kamar yadda TheCable ta tattaro.
Marigayiyar ta kwanta dama ne a ranar Laraba 7 ga watan Faburairu a jihar Legas sakamakon fama da ta yi da ciwon kansa.
Kafin mutuwarta, jarumar ta fito a fina-finai da dama inda ta bayara da gagarumin gudunmawa wurin ilmantarwa da fadakarwar.
Babban Daraktan tace fina-finai, Dakta Shaibu Husseini ne ya sanar da hakan a daren ranar Laraba, 7 ga watan Faburairu.
Asali: Legit.ng