Kashim Shettima Ya Ba Malaman Addini a Najeriya Muhimmiyar Shawara

Kashim Shettima Ya Ba Malaman Addini a Najeriya Muhimmiyar Shawara

  • Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya buƙaci malaman addini da su mayar da hankali wajen kawo zaman lafiya tsakanin ƴan Najeriya
  • Mataimakin shugaban ƙasan dai ya yi wannan kiran ne a wajen taron Mauludin ƙasa karo na 38 a birnin tarayya Abuja
  • Shettima ya kuma buƙace su da su kasance masu ƙoƙarin ganin sun ɗora mabiyansu kan hanyar yin haƙuri da juna

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya buƙaci malaman addini da su zama masu hankalta tare da ƙoƙarin inganta zaman lafiya a tsakanin ƴan Najeriya.

Shettima ya yi wannan kiran ne a wajen taron Mauludin ƙasa karo na 38 na Sheikh Ibrahim Niass, wanda aka gudanar a filin wasa na Mashood Abiola, Abuja, a ranar Asabar, 10 ga watan Fabrairu, cewar rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Najeriya vs Cote d'Ivoire: Shugaba Tinubu ba zai halarci wasan karshe na AFCON ba, bayanai sun fito

Shettima ya shawarci malaman addini
Kashim Shettima ya shawarci malamin addini a Najeriya Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Wacce shawara Shettima ya ba malaman addini?

Shettima ya ce ya kamata malaman addini da mabiyansu a ƙasar nan su riƙa ƙoƙarin fahimtar juna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Fiye da kowane lokaci, muna kira gare ku da ku kasance muryar da za ta cike giɓin da ke tsakanin ilimi da jahilci, tsakanin gaskiya da ɓarna."

Mataimakin shugaban ƙasan ya ƙara da cewa:

"Domin yin koyi da fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) da gaske, dole ne mu cika umarni mai kyau na kasancewa mafi kyawun mutane ta hanyar kawo fa'ida ga jama'armu."

Ya yi nuni da cewa haƙuri da juna da haɗin kai na da muhimmanci wajen mayar da Najeriya ƙasa mai bayar damammaki ga kowa.

"Wannan tunani yana da muhimmanci don cika alkawarinmu na gina al’umma mai dunƙulewa da ci gaba.
"Duk matsayin da mutum ya kai a ɓangaren addini ko ƙabilanci, gaskiyar da ba za a iya musantawa ba ita ce, babu wani daga cikinmu da ya tsira daga illar hargitsi, talauci ko rashin tsaro."

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta shiga sabuwar matsala kan tuhumar tsohon gwamna, bayanai sun fito

Jaridar Daily Trust ta ce Shettima ya kuma buƙaci shugabannin da su sabunta alƙawarinsu na yi wa jama'a hidima.

Shettima Ya Faɗi Dalilin Matsalar Rashin Tsaro a Arewa

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana dalilin da ya sa ake samun matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya.

Mataimakin shugaban ƙasan ya bayyana cewa matsalar cin hanci da rashawa a tsakanin jagorori, ita ce tushen matsalar rashin tsaro a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel