Manyan Labarai A Yau
Majalisar dattawa ta amince da bukatar da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar a gabanta kan wasu nade-nade da ya yi a wasu hukumomin gwamnatin tarayya.
Primate Elijah Ayodele ya yi kira ga gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu da ta mayar da mabuyar 'yan ta'addan Boko Haram su zama gonaki don karfafa tsaro da abinci.
Kungiyar kwadago ta TUC ta janye daga shiga cikin zanga-zangar da kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta shirya gudanarwa a fadin kasar nan kan tsadar rayuwa.
An samu sauyi a jerin manyan masu kudin duniya a 2024 inda matsayin Elon Musk da Mark Zuckerberg suka sauya sannan biloniyan Faransa ya shige gaba.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya shiga ganawar sirri da shugabannin kungiyoyin kwadago a jihar kan yajin aikin sai baba ta gani da suka shiga.
Gwamnatin jihar Ondo karkashin jagorancin Gwamna Lucky Aiyedatiwa, ta ayyana hutun kwana biyu domin gudanar da jana'izar tsohon gwamnan jihar, Akeredolu.
An samu tashin hankali a garin Dutse da ke jihar Jigawa biyo bayan gano gawar wata mata ‘yar shekara mai suna Esther Adekanla wadda aka fi sani da Hadiza Nakowa.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bayyana halin Shugaba Tinubu wanda mafi yawan 'yan Najeriya ba su sani ba, inda ya gadi abin da ya kawo yunwa kasa.
Tsohon shugaban Najeriya Janar Yakubu Gowon, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi hakuri da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu. Gowon ya gana da Tinubu a fadar shugaban kasa.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari