Sabuwar Rigima Ta Barke a Tsakanin Kungiyoyin Kwadago Na TUC da NLC Kan Abu 1, Bayanai Sun Fito

Sabuwar Rigima Ta Barke a Tsakanin Kungiyoyin Kwadago Na TUC da NLC Kan Abu 1, Bayanai Sun Fito

  • Ana saura ƴan kwanaki kaɗan a gudanar da zanga-zangar da ƙungiyar NLC ta shirya, ƙungiyar TUC ta janye daga shiga zanga-zangar
  • Ƙungiyar ta TUC ta bayyana cewa ba a yi shawara da ita ba kafin ɗaukar matakin gudanar da zanga-zangar a faɗin ƙasar nan
  • Ƙungiyar ƙwadago ta NLC dai ta shirya gudanar da zanga-zanga ce ta kwanaki biyu domin adawa da halin da tattalin arziƙin ƙasar nan yake ciki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - A wani sabon salo, ƙungiyar ƙwadago ta TUC ta janye daga shiga zanga-zanga ta kwanaki biyu da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta shirya a faɗin ƙasar nan.

An dai shirya zanga-zangar ne domin nuna rashin amincewa da taɓarɓarewar tattalin arziƙi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Akpabio ya samu matsala da 'yan Najeriya kan abu 1 tak

TUC ta fasa shiga zanga-zanga
Kungiyar TUC ta janye daga shiga zanga-zanga Hoto: @NLCHeadquarters, @Naija_PR
Asali: Twitter

Mataimakin shugaban TUC, Tommy Etim, ya shaidawa jaridar The Punch a wani rahoto da aka buga a anar Alhamis, 22 ga watan Fabrairu, matsayin ƙungiyar kan zanga-zangar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa TUC ta fasa shiga zanga-zangar?

Ya bayyana cewa yanke shawarar yin zanga-zanga a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairu kamar yadda NLC ta sanar, ba dukkanin ƙungiyoyin biyu suka ɗauka ba.

Da yake tabbatar da sabon matsayin na TUC, Etim ya bayyana cewa:

"Ba za mu iya shiga zanga-zangar ba saboda ba a ɗauki matakin a tare ba. A bayyane yake cewa bisa ga wasiƙar, babu yadda za a yi mu shiga zanga-zangar.”

Hakazalika, Nuhu Toro, babban sakataren TUC, a cikin wata wasiƙa, ya caccaki tsarin da ƙungiyar NLC ta ɗauka wajen zaɓar ranakun zanga-zangar, rahoton Blueprint ya tabbatar.

TUC ta koka kan halin shugaban NLC

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Hukumar DSS ta gargadi kungiyoyin kwadago kan gudanar da zanga-zanga, ta fadi dalili

TUC ta yi ƙorafin cewa wannan shi ne karo na uku da shugaban NLC, Joe Ajaero, zai ɗauki mataki ba na bai ɗaya ba.

Wani ɓangare na wasikar TUC na cewa:

"Muna so mu bayyana cewa irin wannan mataki ba na bai ɗaya ba, ya saɓa wa ƙa'idojin fahimtar juna da haɗin gwiwarmu.
"Muna kira gare ku da ku sake yin la’akari da tsarin ku, kuma ku shiga tattaunawa mai ma’ana tare da dukkan ɓangarorin zuwa nan gaba, kamar yadda a ko da yaushe za mu yi irin haka idan buƙatar hakan ta taso".

DSS Ta Gargaɗi NLC Kan Zanga-Zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar ƴan sandan farin kaya ta DSS ta aike da gargaɗi ga ƙungiyar ƙwadago kan zanga-zangar da ta shirya gudanarwa.

Hukumar DSS ta bayyana cewa ta gano shirin wasu ɓata gari na yin amfani da zanga-zangar domin kawo rikici da tashin hankali ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel