Gwamnati Ta Ayyana Hutun Kwana 2, Bayanai Sun Fito

Gwamnati Ta Ayyana Hutun Kwana 2, Bayanai Sun Fito

  • Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya ayyana ranakun Alhamis, 22 ga watan Fabrairu da Juma’a, 23 ga watan Fabrairu a matsayin ranakun hutu a jihar
  • Aiyedatiwa ya bayyana cewa an ayyana ranakun hutun ne domin karrama ubangidansa, marigayi Rotimi Akeredolu
  • Akeredolu ya yi bankwana da duniya ne a watan Disamban 2023, a ƙasar Jamus, bayan ya yi fama da cutar daji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Akure, jihar Ondo - Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya ayyana ranakun Alhamis, 22 ga watan Fabrairu da Juma’a, 23 ga Fabrairu, 2024, a matsayin ranakun hutu a jihar domin karrama marigayi Gwamna Rotimi Akeredolu.

Kwanaki biyun da babu aiki, a cewar Ebenezer Adeniyan, babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan, za su ba al’ummar jihar Ondo damar shiga ayyukan jana’izar marigayi tsohon gwamnan, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Kujerar Ministan Tinubu ta fara tangal-tangal yayin da aka tono abinda ya yi a zaben 2023

An bada hutun kwana biyu a Ondo
Bayan rasuwar Akeredolu, Aiyedatiwa ya maye gurbinsa Hoto: Lucky Aiyedatiwa
Asali: Facebook

Rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da hakan a ranar Talata, 20 ga watan Fabrairun 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe Akeredolu ya rasu?

Idan ba ku manta ba dai Akeredolu ya rasu ne a ranar 27 ga watan Disamba, 2023, kuma za a yi jana'izarsa a ranar Juma'a 23 ga watan Fabrairu a garin Owo, mahaifar sa, kamar yadda iyalansa suka fitar da shirin jana'izarsa.

Akeredolu, mai shekaru 67, ya rasu ne a wani asibitin ƙasar Jamus bayan ya shafe tsawon lokaci yana fama da cutar daji.

Bayan rasuwarsa, Aiyedatiwa wanda shine mataimakinsa ya zama gwamnan jihar.

Babban alƙalin jihar, Olusegun Odunsola ne ya rantsar da Aiyedatiwa, a wani taron da aka gudanar a ofishin gwamna, a Alagbaka, Akure.

Gwamnan mai ci da kyar ya tsallake rijiya da baya kan ƙoƙarin tsige shi a shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Rikici ya shigowa ‘yan APC, an aikawa Shugaban kasa korafin sabon Gwamna

Haka kuma sai da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya shiga tsakani domin kwantar da wutar rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar.

An Rantsar da Sabon Mataimakin Gwamnan Ondo

A baya rahoto ya zo cewa an rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar Ondo, Dakta Olaide Adelami bayan naɗin da Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya yi masa.

Adelaimi ya kama rantsuwar aiki ne bayan majalisar dokokin jihar ta tantance shi tare da amincewa da naɗin da aka yi masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel