“Idan Ka Tsaya Matsalarka Ce”: DirebaYa Tuka Mota Babu Tayar Baya, Ya Kwaso Gudu a Bidiyo

“Idan Ka Tsaya Matsalarka Ce”: DirebaYa Tuka Mota Babu Tayar Baya, Ya Kwaso Gudu a Bidiyo

  • Wani mai amfani da TikTok ya yada bidiyon wani direba da ke tuka motarsa a babban titi ba tare da tayar baya guda daya ba
  • A cewar 'dan TikTok din, watakila direban motar ya kasance a wurin da ba zai iya tsayawa don gyara motar tasa bane
  • Wasu sun yi tunanin cewa watakila direban ya kasance a Legas ne, inda mutum ba zai iya tsayawa a wasu yankuna ba saboda tsoron 'yan jagaliya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jama'a sun yi cece-kuce kan bidiyon wani mutum da ke tuka motarsa ba tare da tayar baya guda daya ba.

A cikin bidiyon, ana iya ganin mutumin yana tuka motar da tayoyi uku maimakon guda hudu.

Wani mutum ya tuka mota da tayoyi uku a titi
“Idan Ka Tsaya Matsalarka Ce”: Wani Mutumi Ya Tuka Mota Babu Tayar Baya, Ya Kwaso Gudu a Bidiyo Hoto: TikTok/@jay_scotch_autos.
Asali: TikTok

A cikin bidiyon da @jay_scotch_autos ya wallafa, ya bayyana cewa watakila direban ya tsinci kansa ne a cikin wani mawuyacin yanayi.

Kara karanta wannan

Ana karbar kebura: Bidiyon wani matashi da ke shan garin kwaki da man ja ya girgiza intanet

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin da mutane suka yi kan bidiyon ya nuna cewa watakila direban na tuki ne a Legas, inda ba zai iya tsayawa a wasu yankuna ba.

Martanin na cewa idan direban ya tsaya a wasu yankuna don gyara tayarsa 'yan jagaliya na iya mamaye shi don ya biya kudi, don haka ya zabi tuki da karfen motar.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kan bidiyon

@user8199810091324 ya yi martani:

"Idan ka taya matsalarka ce."

@Akran Larry ya ce:

"Ya fi ace wadannan samarin su zo su same ka."

@Akpuruka 1 ya ce:

"Hikima. wannan ne mafita guda daya. Ga wadanda suka san hanyar."

@future ya yi martani:

"Na rantse nine wannan."

@Weston of AAUA ya ce:

"Ta yiwu barawo ne faaa. Wanda ke guduwa da motar wani."

@jane-omah ya ce:

"Idan ka tsaya za ka biya 'yan daba kudi."'

Kara karanta wannan

Tsadar siminti: Yadda wasu maza 2 suka dukufa ginin gida babu siminti, bidiyon ya haddasa cece-kuce

An aiki direba da abinci, ya cinye

A wani labarin, wata matashiya yar Najeriya mai suna @ozzyetomi ta je dandalin Twitter domin ba da labarin wani a al'amari mai ban mamaki da ya faru tsakanin wata da direban Uber.

Dirama ya barke bayan kawarta ta tura direban Uber ya karbo mata abincin Sallah daga wajen wata kawarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng