Manyan Labarai A Yau
An bayyana dalilin da yasa wata dalibar karatun jinya a mataki na 3 a jihar Ogun ta dauki ranta da kanta. Gwamnatin jihar ta yi kakkausan gargadi.
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang ya aike da sakon ta'aziyya kan kisan da aka yi wa sakataren yada labarai na jam'iyyar APC a jihar. Ya ba jami'an tsaro umarni.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai sabon hari a jihar Benue inda suka tafka mummunar ta'asa. 'Yan bindigan sun salwantar da rai tare da kona gidaje.
Hukumar karbar korafe-korafen jama'a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ta bude rumbunan da ake zargin suna boye kayan abinci da ta rufe a jihar.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bada umurnin a biya bashin naira miliyan 324.35 ga Hukumar Rarraba Lantarki na Abuja, AEDC, da ake bin Gidan Gwamnati.
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu Sokoto, ya amince da karin kaso 100% na alawus-alawus din da ake biyan matasa masu yi wa kasa hidima a jihar Sokoto.
Tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung, ya caccaki gwamnatin Shugaba Tinubu kan yadda take dora alhakin halin da ake ciki kan gwamnatin Buhari.
Tsohon gwamnan jihar Ogun kuma Sanatan Ogun ta Gabas, Gbenga Daniel, ya roki 'yan Najeriya da su kara hakuri da gwamnatin Tinubu kan halin da ake ciki a kasar nan.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa za ta kayyade farashin abinci a kasar saboda hauhawan farashin kaya a kasar, musamman ma kayan abinci da sauransu.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari