Sanatan APC Ya Fallasa Yadda Gwamnatin Tarayya Ke Cin Gajiyar Faduwar Darajar Naira

Sanatan APC Ya Fallasa Yadda Gwamnatin Tarayya Ke Cin Gajiyar Faduwar Darajar Naira

  • Sanata Ali Ndume ya bayyana yadda gwamnatin tarayya ke cin moriyar faɗuwar darajar Naira a kan Dala
  • Sanatan ya bayyana cewa yayin da farashin Dala ke ƙara tsada hakan na nufin gwamnatin tarayya za ta ƙara samun kuɗaɗen shiga idan ta mayar da Dala zuwa Naira
  • Ya yi nuni da cewa hakan zai ba gwamnatin damar samun kuɗin gudanar da kasafin kuɗinta na shekarar 2024 tun da a Dala ta yi shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Sanata Ali Ndume, ya yi bayanin cewa gwamnatin tarayya na cin gajiyar faduwar darajar Naira a kan Dala.

Ndume yana magana ne kan dalilin da yasa darajar Naira ke ci gaba da faduwa a kan Dala.

Kara karanta wannan

Akpabio ya samu matsala da 'yan Najeriya kan abu 1 tak

Ndume ya yi magana kan faduwar darajar Naira
Sanata Ndume ya ce FG na cin moriyar faduwar darajar Naira Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Ali Ndume
Asali: Facebook

Ndume ya ce maimakon yin asara a faɗuwar darajar Naira a kan Dala, Gwamnatin Tarayya na samun ƙarin kuɗaɗen shiga don kasafin kuɗinta na 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Channels tv a ranar Laraba.

Ta wacce hanya FG ke amfana da faɗuwar darajar Naira?

Sanatan ya bayyana cewa gwamnati za ta samu ƙarin Naira da za ta kashe wajen gudanar da ayyukanta yayin da darajar Dala ta ƙaru.

A cewar Ndume, kasafin kuɗin shekarar 2024 da aka gabatar a watan Nuwamba, ya dogara ne kacokan kan Daloli don samun kuɗin shiga, ganin cewa kaso mai tsoka na kuɗaɗen shigar da gwamnati ke samu na zuwa daga fitar da ɗanyen mai, wanda farashinsa ya ke a Dala.

A kalamansa:

"Don haka idan muna samun kuɗinmu a Daloli sannan darajar Dala ta yi sama, hakan na nufin za mu samu Naira mai yawa kan abin da muke kashewa, saboda ba a Dala muke kashewa ba, yayin da muke samun kuɗaɗen shirgar mu a Dala.

Kara karanta wannan

Sanata Sani ya fadi mafita 1 da Musulmi da Kiristoci zasu runguma domin farfado da naira

"Tabbas gaskiya ne darajar Naira kan Dala ta faɗi warwas amma muna sayar da babban abin da yake samar mana da kuɗaɗen shiga a Dala. Hakan na nufin duk Dala da muka samu yanzu darajarta tana daidai da farashin Naira-Dala na yanzu.
"Don haka idan ka yi nazari sosai, hakan yana na nufin idan ka haɗa komai da komai, muna iya samun ƙarin kuɗi don kasafin kuɗin mu. Don haka Najeriya cin gajiyar tashin farashin Dala zuwa Naira take yi."

Ndume Ya Kawo Dabarar Samun Abinci

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanatan Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume ya faɗi hanyar da talaka zai samu abinci a ƙasar nan.

Sanatan ya bayyana cewa da shi takwarorinsa a majalisar dattawa sun kawo ƙudurin da zai ba ma'aikata, waɗanɗa albashinsu bai kai ba damar samun abinvo a kasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng