Manyan Labarai A Yau
Bayan shafe tsawon shekaru 13 a banki, wata mata ta ajiye aikinta sannan ta koma ga noma. Ta mayar da gidanta wajen kiwon kifi da kaji kuma tana samu sosai.
Rundunar sojojin Najeriya ta Operation Hadarin Daji (OPHD) ta sanar da samu nasara kan yadda ta'addan da suka addabi jihar Zamfara da ke shiyyar Arewa maso Yamma.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya isa jihar Ondo da ke yankin Kudu maso Yammacin Najeriya. Shugaban kasan zai yi ta'aziyyar tsohon gwamnan jihar.
Gwamnatin tarayya ta bayyana abubuwan da ake bukata domin samun tallafin kudi na N25,000 duk wata, wanda za a ba iyalai miliyan 15 a fadin kasar nan.
An kaddamar da wata kotun soji a jihar Plateau wacce za ta saurari shari'ar da ake yi wa wasu sojoji 17 kan zargin sayar da makamainda wasu laifukan.
Babban lauya a Najeriya, Mike Ozekhome, ya yi hasashen cewa idan aka ci gaba da tafiya a haka, darajar Naira sai ta fadi kasa zuwa N4000/$1 kafin karshen 2024.
Majalisar wakilai ta hannun kwamitin asusun jama'a ta yi barazanar aikewa da sammacin kamu kan gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso.
Tsohon jigo a jam'iyyar PDP, Deji Adeyanju, ya nuna takaicinsa kan matakin da kungiyar kwadago ta kasa ta dauka na dakatar da zanga-zangar da fara.
Kungiyar Kwadago ta Najeriya ta sanar da dakatar da zanga-zangar kwanaki biyu a fadin kasar wadda ta fara a ranar Talata. An bayyana babban dalilin dakatarwar.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari