Su Wanene Suka Cancanci Tallafin N25,000 Duk Wata Na Gwamnatin Tarayya da Yadda Za a Samu?

Su Wanene Suka Cancanci Tallafin N25,000 Duk Wata Na Gwamnatin Tarayya da Yadda Za a Samu?

  • Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da shirinta na bayar da tallafin kuɗaɗe ga ƴan Najeriya
  • Da yake tabbatar da hakan, ministan kuɗi, Wale Edun, ya bayyana cewa an ƙara ƴan Najeriya miliyan 12 a matsayin waɗanda za su amfana da shirin
  • A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, Wale Edun ya fitar da sharuɗɗan da za a bi domin cancanta wajen samun tallafin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin Najeriya ta bayyana abubuwan da ake buƙata domin shirin bayar da tallafin kuɗaɗe ga iyalai miliyan 15 da ke fama da matsalolin tattalin arziƙi.

Shugaba Bola Tinubu ya ji koke-koken ƴan Najeriya game da hauhawar farashin kayayyakin abinci, ya kuma tabbatar da aniyar dawo da tallafin kuɗaɗe ga mabuƙata da iyalai.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: An yi hasashen Dala za ta kai N4000 kafin karshen 2024, an fadi dlalili

FG ta dawo da tallafin N25,000
FG ta sanar da sake dawo da bayar da tallafin kudade Hoto: Wale Edun
Asali: UGC

FG ta amince da ƙarin masu cin gajiya mutum 12m

Kafin dakatar da shirin bayar da tallafin kuɗaɗen a watannin baya, aƙalla ƴan Najeriya miliyan uku ne suka ci gajiyar shirin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda BBC Pidgin ta ruwaito, gwamnatin tarayya ta ƙara adadin wadanda suka amfana zuwa miliyan 15 saboda tsadar rayuwa da kuma tabarbarewar tattalin arziƙi.

A halin da ake ciki kuma, ministan kuɗi, Wale Edun, a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels TV, ya lissafo abubuwan da ake buƙata domin cin gajiyar tallafin.

Me ake buƙata domin samun tallafin?

Ya ce ana buƙatar mutum ya mallaki lambar shaida ta ƙasa (NIN), BVN tare da samun damar yin amfani da wayar hannu.

Ministan ya ce an yi hakan ne domin tabbatar da cewa kudaden sun isa ga mutanen da suka dace domin kaucewa samun matsala a rabon.

Kara karanta wannan

"A ƙara haƙuri" Abu 1 da aka buƙaci Shugaba Tinubu ya yi domin magance tsadar rayuwa a Najeriya

A tafiyar da ya yi a Akwa Ibom kwanan nan, ministan ya sake nanata haka.

Kamar yadda Channels TV ta ruwaito, ya ce:

"Kwamitin shugaban ƙasa kan shirye-shiryen jin ƙai sun shirya don zuwa ga shugaban ƙasa tare da shawarwarin cikin gida don sake fara biyan kuɗi kai tsaye ga matalauta da masu rauni. Ana yin duk mai yiwuwa don rage raɗaɗin da ake ciki.
"Mun san cewa kusan mutane miliyan uku ne suka amfana a yanzu, amma idan aka yi la’akari da hauhawar farashi, akwai akwai ƙarin iyalai miliyan 12, da za su ci gajiyar wannan tsarin."

FG Za Ta Fara Ba Matasa Alawus

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta shirya fara ba matasa marasa aikin yi alawus domin rage raɗaɗi.

Gwamnatin dai za ta bayar da tallafin ne ga matasa masu kwalin digiri ko na kwalejin ilmi domin ciro su daga halin ƙunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel