Yadda Ma’aikaciyar Banki Ta Ajiye Aikinta Na Shekaru 13, Ta Kama Sana’ar Da ke Kawo Mata Kudi Kullun

Yadda Ma’aikaciyar Banki Ta Ajiye Aikinta Na Shekaru 13, Ta Kama Sana’ar Da ke Kawo Mata Kudi Kullun

  • Sana'ar kiwo da aka fara shi domin samun na goro ya habbaka ya zama ginshiki ga wata tsohuwar ma'aikaciyar banki
  • Gaba daya abin ya fara ne lokacin kullen annobar korona, wanda ya sa mutane zaman gida, ciki kuwa harda tsohuwar ma'aikaciyar bankin da yaranta
  • Ta mayar da gidanta ya zama wajen kiwon kifi da kaji sannan ta ajiye aikinta na banki bayan ganin alfanun da ke cikin harkar noma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wata mata 'yar Najeriya wacce ta bar aiki a matsayin ma'aikaciyar banki ta rungumi noma ta ja hankalin mutane da dama da labarinta.

Wani 'dan gajeren bidiyo na sana'ar kiwon da take yi ya yi bayanin cewa ta mayar da gidanta ya zama wajen da take kiwon kifi da kaji lokacin annobar Korona, wanda ya yi sanadiyar yi wa mutane kulle.

Kara karanta wannan

"Akwai yunwa a kasar": Gwamnan PDP ya shiga zanga-zangar 'yan kwadago a jiharsa

Ma'aikaciyar banki ta zama mai gidan gona
Yadda Ma’aikaciyar Banki Ta Ajiye Aikinta Na Shekaru 13, Ta Kama Sana’a Mai Ban Mamaki a Bidiyo Hoto: @mechidykefarms
Asali: TikTok

A cewar bidiyon, dalilinta na shiga harkar noma don taimakawa iyalinta da hanyar samun kudaden shiga ne a lokacin kullen kasancewar basu san tsawon lokacin da zai dauka ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, bayan watanni uku, matar ta ga cewa akwai ci sosai a harkar noma don haka ta yanke shawarar ajiye aikin da take na banki, wanda shine ya kawo karshen aikinta na shekaru 13.

Gonar Mechidyke na samar da kiret 30 na kwai

A cewar matar, sun fara ne da kajin turawa guda 25 da kananan kifaye 50 amma a yanzu, suna da kaji masu kwai guda 3,000 da ramin kifi dauke da kifaye 5,000.

An rahoto cewa kaji masu kwai da ke gonar Mechidyke suna samar da kwai a kalla kiret 30 a kullun. Kan dalilinsu na mayar da shi sana'ar gidansu, tsohuwar ma'aikaciyar bankin ta ce:

Kara karanta wannan

Wani uba ya yi watsi da 'yan kai amarya, ya yi wa diyarsa rakiya zuwa dakin mijinta da kansa, bidiyo

"Mun gano cewa akwai sha'awar abin tsakanin yaran da ni."

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Your Trusted Lagos Realtor ya ce:

"Ka yi tunanin ace baka biyan 150 kudin kwai a yanzu lallai 2020 ya sauya rayuwar wasu mutane zuwa mai kyau."

parcel ta ce:

"Don Allah mana, ta yaya kaji 3000 ke samar maki da akalla kiret 30 na kwai, asara tsantsa. Kamata ya yi ace kaji 3000 suna samar da akalla kwai kiret 80 zuwa 90."

HBK ta ce:

"Gona mai kaji 5000 ba karamin abu bane fa. kina bukatar akalla naira miliyan 4 don ciyar da su tsawon watanni 4 zuwa 6. Watakila tana da isasshen jari."

SerahAlexis ta ce:

"Ta ajiye aikinta a matsayin ma'aikaciyar banki wata rana zai zama ni, na gaji."

Manoma sun fara barin kiwon kaji

A wani labarin, mun kawo a baya cewa 'yan Najeriya za su kara fuskantar tsadar kwai yayin da manoman kwai ke fama da hauhawan farashin abubuwa.

Tsohon sakataren kungiyar masu kiwon kaji na Najeriya (PAN) reshen jihar Lagas, Olufemi Stephens, ya koka kan yanayin tsadar abincin kaji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel