Labaran Soyayya
Wani magidanci mai shekaru 83 a duniya yayi aure a karo na 11. Yana da yara 126 kuma yace yana da kudi, lafiya da ta kwakwalwa da zai iya rike matan auren.
Wani ango da amaryarsa sun yadu a TikTok bayan bidiyo ya nuno su suna keta jeji a kafa zuwa wajen daurin aurensu. Mijin ya taya matar tasa rike rigarta ta baya.
David Baerten ya ce ya shiga damuwa sosai saboda yadda danginsa suka yanke hulda da shi don haka ya yi karyan ya mutu saboda ya koya masu darasi kan zumunci.
Wani matashi dan Najeriya ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ya angwance da sahibarsa tsohuwar baturiya da ta girme masa. Hotunan aurensu sun yadu.
Wata matashiya da ta auri mai nakasa ta wallafa tsoffin hotunansa don nuna yadda yabsauya bayan shekaru 10, kuma jama’a da dama sun yaba tsantsar kyawunsa.
Wani bincike da aka gudanar a ƙasar Burtaniya ya nuna cewa da sanyin safe ne lokacin mafi kyau ma'aurata su kwanta da juna su ji daɗi, yana kara farin ciki.
Wani magidanci ya koka kan yadda matarsa da suka shekara shida suna zaman aure ta tafi ta bar shi bayan ya samu hatsari. Har ta ƴaƴansa sai da ta kwashe su.
Wani matashi ya auri mata biyu a tare, bayan auren su, sun samu juna biyu a lokaci ɗaya kuma suka haihu a lokaci ɗaya, mutane sun cika da mamaki kan bidiyon.
Wata matashiya yar Najeriya, Hazel, wacce aurenta ya mutu bayan watanni bakwai ta garzaya Facebook don caccakar tsohon mijinta wanda ta ce yana kunyar nuna ta.
Labaran Soyayya
Samu kari