"Wannan Auren Dole Ne": Tashin Hankali Bayan Amarya Ta Ki Rungumar Ango, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

"Wannan Auren Dole Ne": Tashin Hankali Bayan Amarya Ta Ki Rungumar Ango, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

  • Wata amarya ta janyo cece-kuce a wajen ɗaurin auren ta bayan ta ƙi yarda angonta ya rungume ta
  • Amaryar ta naɗe hannayenta sannan ta ɗaure fuska lokacin da angon ya miƙa hannayen sa yana son ya rungume ta
  • Bidiyon wanda ya yaɗu sosai ya janyo cece-kuce, inda wasu da yawa suke cewa auren dole ne aka yi mata

Wani bidiyo da ya yaɗu na wani wajen ɗaurin aure ya nuna lokacin da wata amarya ta ƙi yarda ta rungume angon ta.

Amaryar wacce ba ta cikin farin ciki ta ƙi yarda angon ya rungume ta inda ta maƙale hannayen ta lokacin da ya ke ƙoƙarin rungumo ta.

Amarya ta ki yarda ta rungume angonta
Amarya ta ki yarda angonta ya rungume ta Hoto: @messisesay
Asali: TikTok

Ganin cewa ba za ta yarda ya rungume ta ba, sai angon ya matsa kusa da ita inda ya rungumo ta da ƙarfin tsiya, sannan ya haɗa mata da sumbata.

Kara karanta wannan

Abun Kallo: Wata Amarya Ta Fusata Ta Hukunta Mijinta Kan Laifi 1, Bidiyon Ya Girgiza Mutane

Duk da haka dai amargar ta ƙi sakin fuska ta yi murmushi. Bakin da suka halarci wajen sun kewaye su da kyamarori suna ɗaukar abinda ke wakana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan soshiyal midiya sun yi mahawara akai

Bidiyon wanda aka ɗora a TikTok, ya yaɗu sosai inda sama da mutum 400k suka kalla, yayin da yawa daga ciki ke da ra'ayin cewa amaryar ba ta maraba da auren.

Ga kaɗan daga cikin ra'ayoyin ƴan soshiyal midiya kan bidiyon:

Greatness Doro ta rubuta:

"Ba wai ba ta farin ciki bane ooo mutanen da ke zolayar ta ne suka ɓata mata rai."

Dehain ya rubuta:

"Ƴar'uwa benard ba ta murna ko kaɗan, ta yi kama da tilas akai mata ta yi auren."

bulelwa030khwezi ya rubuta:

"Tabbas daga gani nan babu wata soyayya."

user3775421787614 ya rubuta:

Kara karanta wannan

Abin Al'ajabi a Najeriya: Wani Bawan Allah Ya Sha Mamakin Kuɗin Da Ya Samu Bayan Ya Roki Allah $100m

"Yayin da ku ke yi wa ƙasar ku addu'a... ku sanya mutumin nan cikin addu'o'in ku."

Pretty Dazzy ta rubuta:

"Wannan auren dole ne ko ku yarda ko ka da ku yarda."

user8293510191915 ya rubuta:

"Lokacin da ba ka son yin aure amma kana son burge ƴan'uwan ka."

Magidanci Ya Yiwa Mai Koyon Aiki Wajen Matarsa Ciki

A wani labarin na daban kuma, wani magidanci ya biye wa zuciya ya aikata aikin dana sani. Magidancin dai ya lallaɓa ya yiwa mai koyon aiki wajen matarsa ciki.

Magidancin ya kuma koma yana kare ta duk da wannan taɓargazar da ya aikata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel