Labaran garkuwa da mutane
Wasu masu zuwa coci ɗaukar karatun Littafi Mai Tsarki (Bible) sun faɗa hannun ƴan bindiga a hanyarsu ta komawa gida a Akure ta Yamma a jihar Ondo.
'Yan bindiga sun kai hari unguwar Grow Himes da ke Chikakore a Kubwa da ke birnin tarayya Abuja. Sun yi artabu da 'yan sanda kuma sun sace mutane da dama.
Dakarun sojin Najeriya sun farmaki dan bindiga Kachalla Murtala a jihar Katsina. An ceto wata matar da ta shafe kwana 70 a dajin wajen 'yan bindiga masu garkuwa.
An samu Hamdiyya Sidi Shafif a dajin Zamfara bayan sace ta a Sokoto. Ta fadi yadda aka sace ta a Sokoto da yadda aka mata allura a dajin Zamfara saboda rashin lafiya
Wasu miyagun ƴan bindiga sun kaddanar da hare-hare a kauyukan jihar Benuwai da ke Arewa ta Tsakiya, sun yi ajalin tsohon shugaban PDP na mazaɓa da wasu mutum 3.
Mutane a wasu yankuna na jihar Zamfara musamman karamar hukumar Kaura na Moda na barin gidajensu da dare su dare da safe saboda tsaron hare hare.
Hukumomi a kasar Saudiyya sun cafke wasu mata biyu da ake zargin iyalan dan bindiga Ado Aliero ne a garin Madina yayin da suka tafi aikin Hajji daga Najeriya.
Jami'an tsaro sun kama wani da ake nema ruwa a jallo bisa zargin garkuwa da mutane a sansanin aikin Hajji da ke Abuja yayin da ake tantance maniyyata.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ƴan bindiga sun sace basarakena jihar Kogi da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya, ƴan sanda sun fara farautarsu domin ceto shi.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari