Bayan Cikar Wa’adi, Majalisar Dattawa Za Ta Sake Duba Batun Tsige Buhari Ranar Talata

Bayan Cikar Wa’adi, Majalisar Dattawa Za Ta Sake Duba Batun Tsige Buhari Ranar Talata

  • Majalisar dattawan Najeriya ta ba shugaban kasa Muhammadu Buhari wa'adin lokacin da zai kawo karshen matsalar tsaro
  • Lokacin da aka dibar masa ya cika, majalisar za ta sake zama a ranar Talata mai zuwa don sake duba batun
  • 'Yan Najeriya da dama, da ma 'yan jam'iyyun adawa da na koka mulkin Buhari kasancewar zaman lafiya ya gagara

FCT, Abuja - Wa'adin makwanni shida da aka dibarwa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya warware matsalolin tsaron Najeriya sun shude, har yanzu abubuwa basu kankama ba.

A cewar rahoton jaridar The Guardian, majalisar dokokin Najeriya za ta sake zama a ranar Talata mai zuwa, 20 ga watan Satumba don sake duba batun tsige shugaban.

Majalisa za ta sake duba batun tsige Buhari ranar Talata mai zuwa
Majalisar dattawa za ta sake duba batun tsige Buhari a cikin makon nan | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Idan baku manta ba, rahotanni sun karade Najeriya a ranar 27 ga watan Yuli cewa, majalisar dattawa ta dago batun tsige Buhari saboda ta'azzarar lamurran tsaro.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa A 2023: Tinubu Na Da Karfin Da Zai Iya Farfado Da Najeriya, Yahaya Bello

Sanatoci sun nuna kin jinin mulkin Buhari

An ruwaito cewa, sanataoci 20 dake goyon bayan batun sun yi gangami a majalisa yayin da Ahmad Lawan, shugaban sanatoci ya yi watsi da kudurin kawo karshen mulkin Buhari saboda lalacewar tsaro a yankuna daban-daban na Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kuma ce, sun fice daga zauren majalisar saboda rashin sauraran batunsu na tada batun tsige shugaban kasa

Shugaban marasa rinjaye, Sanata Philip Aduda na jam'iyyar PDP an ce ya magantu da manema labarai kan wa'adin da aka dibarwa shugaba domin ya kawo karshen rashin tsaro ko a tsige shi.

Ga dai bidiyon lokacin sanatocin ke gangamin nuna adawa da ci gaba da mulkin Buhari:

A bangare guda, gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya bayyana goyon bayansa ga kawo karshen mulki Manjo Muhammadu Buhari mai ritaya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali ga 'yan Najeriya yayin da Buhari yace zai haramta amfani da kananzir

Gwamnan ya yabawa kokari sanatocin bisa tado da wannan babban batu domin ceto Najeriya.

Dama gwamna Ortom ya kware wajen sukar gwamnatin Buhari.

Fitaccen Sanatan APC Daga Arewa Ya Goyi Bayan A Tsige Buhari

A wani labarin, Sanata Elisha Abbo, dan majalisar tarayya daga Adamawa North ya goyi bayan kiran da sanatocin jam'iyyun adawa suka yi na tsige Shugaba Muhammadu Buhari.

Abbo ya bayyana matsayinsa ne kan batun tsige shugaban kasar a wurin taron shugabannin kiristoci na Arewa da aka yi a ranar Juma'a 29 ga watan Yuli a birnin tarayya, Abuja.

Sanatan ya fada wa yan jarida cewa dalilinsa na goyon bayan kiran tsige shugaban kasar shine mummunan halin rashin tsaro da ake ciki a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel