Labaran garkuwa da mutane
An kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane a wani yankin jihar Yobe da ke Arewa maso Gabas. An bayyana yadda aka yi ya shiga hannun jami'an 'yan sanda.
Rundunar Operation Hadarin Daji ta ƙara kubutar da wasu mutane 15 bayan artabu da 'yan bindiga a jihar Zamfara, sun sheke wasu da ciki da yawa yau Litinin.
Bayan sace ɗalibai mata, miyagun 'yan bindiga sun shiga wurin kwanan ma'aikatan gini a jami'ar tarayya da ke Gusau, a jihar Zamfara sun kwace mutane 9.
Wasu tsagerun 'yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da wani babban Fasto da ɗiyarsa a Kalaba, babban birnin jihar Kuros Riba.
Wasu dalibai sun bayyana cewa mahara sun sace abokan karatunsu mata a ɗakunan kwanansu ta hanyar shiga ta tagogi da silin ranar Alhamis da daddare.
Masu garkuwa da mutane sun hari kauyen Dogon Noma da ke Maro, a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, inda suka kashe mutum biyu tare da garkuwa da wasu uku.
Wasu yan bindiga sun tare motocin kamfanin 'Benue Links' mallakin gwamnatin jihar Benuwai, sun yi awon gaba da fasinjoji akalla 10 ranar Lahadin nan.
Masu garkuwa da mutane sun auka gidan ‘dan sanda, sun yi gaba da iyalin jami’in tsaro. Majiyoyi sun shaida cewa masu garkuwa da mutanen sun zo ne da makamai.
Jami'an rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna sun samu nasarar kubutar da mutane 3 da yan bindiga suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Zariya, jihar Ƙaduna.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari