Mahaifiyar Doge Gide Ta Roki Ya Saki ’Yan Matan da Ya Sace a Kwalejin Tarayya da Ke Yauri, Jihar Kebbi

Mahaifiyar Doge Gide Ta Roki Ya Saki ’Yan Matan da Ya Sace a Kwalejin Tarayya da Ke Yauri, Jihar Kebbi

  • Yayin da iyaye ke ci gaba da kuka kan sace 'ya'yansu da aka yi a kwalejin tarayya da ke Yauri a Kebbi, wani batu ya fito
  • Mahaifiyar dan bindiga ta roki danta da ya sako daliban da ya sace ya auri wasu daga ciki saboda wasu dalilai
  • Ana ci gaba da binciko hanyar da za a bi domin kwato daliban da 'yan bindigan suka sace a kwalejin Kebbi

JIhar Kebbi - Har yanzu akwai sauran dalibai mata da ke hannun ‘yan bindigan da suka sace daliban kwalejin tarayya da ke Yauri a jihar Kebbi.

An tattaro cewa, tuni ‘yan bindigan sun aurar da wasu daga cikin daliban, kana wasu sun haihu duk dai a sansanin ‘yan ta’addan.

Iyaye da sauran masu ruwa da tsaki sun yi yunkuri sau da yawa don ganin an kubutar da ‘yan matan, amma hakan bai kai ga nasara ba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Ganduje ya Bayyanawa Buhari Matsayar Kanawa Kan Ziyarar da Zai Kai Jihar

Halin da iyaye ke ciki game da daliban yauri
Mahaifiyar Doge Gide Ta Roki Ya Saki ’Yan Matan da Ya Sace a Kwalejin Tarayya da Ke Yauri, Jihar Kebbi | Hoto: thewhistler.ng
Asali: Facebook

Gwamnati ta gaza yin komai

Abinda duniya ke cewa, wannan gazawa ce ga gwamnatin tarayya da ta jihar Kebbi, ganin cewa su ke rike da amanar yaran da iyayensu ke nesa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

BBC Hausa ta tattauna da daya daga masu ruwa da tsaki a kokarin kubutar da daliban, Kanal Abubakar Dangiwa Umar mai ritaya, wanda tsohon gwamnan Kaduna ne kan batun da ya shafi ‘yan matan.

Kanal ya bayyana cewa, Doge Gide, daya daga cikin shugabannin ‘yan bindigan ya auri daga daga cikin ‘yan matan 11 da suka rage.

Mahaifiyar Dogo Gide ta nemi ya saki daliban

Kanal ya kuma shaida cewa, mahaifiyar kasurgumin dan bindigan ta shawarce shi da ya saki sauran daliban da ke hannunsa.

Kamar dai ya ji batun mahaifiyar tasa, amma ya sanya sharudda, ciki har da kawo makudan kudade na fansa kafin sakin daliban.

Kara karanta wannan

Duk Da Rashin Amincewar Ganduje, Buhari Zai Kai Ziyara Jihar Kano a Gobe Litinin

Da yake bayyana halin da ake ciki, Kanal ya koka da yadda hukumomin tsaro suka ce za su iya ceto daliban, amma suka gaza.

An sha sace dalibai a Arewacin Najeriya, akan ba da kudaden fansa don sako daliban da basu ji ba basu gani ba.

Ba wannan ne karon farko da iyayen 'yan ta'adda a Najeriya ke yin dana-sani ba, a baya mahaifiyar Shekau ta bayyana yadda ya tsoma ta cikin radadi da tashin hankali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel