Labaran garkuwa da mutane
Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta samu nasarar dakile wani yunkuri da 'yan bindiga suka yi na yin garkuwa da mutane. Sun yi musayar wuta tare da fatattakarsu.
Wani sabon ango mai suna Sani yana daga cikin mutane 21 da ‘yan bindiga suka kashe a wata kasuwar mako a garin Madaka, karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.
Rahotanni sun nuna cewa magajin gari da wasu mutane 20 sun ru yayin da ƴan bindiga suka kai farmaki wani kauyen karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.
Gwamnatin Katsina karkashin Malam Dikko Radda tare da dakarun sojin saman Najeriya sun yi nasarar ceto mutane 17 da aka yi garkuwa da su a dajin Jibia.
Gwamnatin tarayya ta fitar da cikakken jerin sunayen mutane da kamfanonin da take zargin suna taimakawa ƴan ta'adda a Najeriya, ciki har da Tukur Mamu.
Wasu tsagerun ƴan bindiga sun tare motar hukumar sufurin jihar Katsina, sun yi awon gaba da gomman fasinjoji a yankin ƙaramar hukumar Kankara ranar Alhamis.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya nuna damuwa kan yadda ake samun karuwar masu ba 'yan bindiga bayanaiɓa kauyukan da ke fama da rashin tsaro.
Asirin wata matar aure ya tonu bayan ta yi garkuwa da kanta tare da karbar kudin fansa N2m daga mijinta tare da raba kudin da saurayinta a Abuja.
'Yan bindigar sun kai farmaki garin Ɓaure da ke ƙaramar hukumar Gusau, jihar Zamfara a yammacin ranar Talata, lokacin da al'ummar garin ke shirin buɗa baki.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari