Sojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga 3 Tare da Ceto Mutane 16 da Suka Yi Garkuwa da Su a Kaduna

Sojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga 3 Tare da Ceto Mutane 16 da Suka Yi Garkuwa da Su a Kaduna

  • Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar hallaka wasu ‘yan bindigan da suka addabi jama’a a jihar Kaduna
  • Sojoji sun ceto wasu mutum 16 da ‘yan bindigan suka sace a wata karamar hukumar jihar ta Kaduna da ke Arewa maso Yamma
  • Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin da ke fama da yawaitar hare-haren ‘yan bindiga, musamman a shekarunan nan

Jihar Kaduna - Dakarun sojin Najeriya karkashin rundunar Operation Forest Sanity sun ceto wasu mutane 16 da ‘yan bindiga suka sace a kananan hukumomin Birnin Gwari da Igabi a jihar Kaduna.

Hakazalika, rahoton da muke samu ya bayyana cewam sojojin sun yi nasarar hallaka ‘yan bindiga uku a ayyukan da suka yi a yankunan, Punch ta ruwaito.

Wannan na fitowa ne daga bakin kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata 24 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Bayan kazamin fada da ISWAP, daruruwan 'yan Boko Haram sun mika wuya ga sojin Najeriya

Yadda 'yan bindiga suka sha kashi a hannun sojoji a Kaduna
Sojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga 3 Tare da Ceto Mutane 16 da Suka Yi Garkuwa da Su a Kaduna | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A cewar sanarwar tasa, tuni aka debe wasu daga cikin wadanda aka ceto din zuwa asibiti da ke kusa a jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An kwato makamai da babura

A cewar Aruwan, kadan daga kayayyakin da aka kwato daga hannun ‘yan ta’addan sun hada da bindiga AK-47 guda daya, wata bindigar gida daya, kayan fashewa, radiyon oba-oba da babura guda 10.

A cewar sanarwar, sojoji sun amsa kiran gaggawa game da harin ‘yan bindiga a Udawa-Manini a karamar hukumar Birnin Gwari, inda suka dakile hari tare da ceto mutane 15 nan take, daya ya samu raunuka.

Haka nan, dakarun sun yi aiki irin wancan a garin Gonan Doctor da ke karamar hukumar Igabi a jihar, inda suka yi kwanton bauna a yankin Maraban Huda, Channels Tv ta ruwaito.

Gwamna ya yabawa sojoji

Kwamishinan ya ce gwamna El-Rufai ya yaba da wannan aikin, ya kuma karfafawa jami’an tsaro gwiwa bisa aikin kakkabe ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Kaico: An shiga tashin hankali, 'yan bindiga sun sace amare 2 da mutum 47 a jihar Arewa

Ya ce gwamna ya godewa irin namijin aikin da suke yi, tare da yin addu’ar Allah ya ba wadanda suka raunata lafiya cikin gaggawa.

Baya ga nasarar sojoji a Arewa maso Yamma, ana ci gaba da kai 'yan Boko Haram kasa a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan.

Wasu da yawa ne suka mika wuya bayan samun matsala da abokan ta'addancinsu na ISWAP a jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.