Jihar Kano
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya nada dan takarar gwamna a jihar Kano a karkashin jam'iyyar APC, Nasiru Gawuna mukamin shugaban kwamitin gudanarwa na Jami'ar Bayero.
Tun bayan nada shi Sarkin Kano na 16, a karon farko Malam Muhammadu Sanusi II ya yi magana kan halin da kasar nan ke ciki da ma hanyoyin da za a kawo gyara.
Babbar Kotun Tarayya ta ci tarar gwamnatin Kano N10m bayan umarnin cafke Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero inda ta ce hakan ya saba dokar ƴancin ɗan Adam.
Hukumar tsaron fararen hula ta NSCDC ta bayyana cewa ta kammala shirye-shiryen tabbatar da tsaron dukiya da rayukan jama’a a domin gudanar da bikin sallah.
Yayin da kotu ta yi hukunci kan korafin Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, dubban jama'a sun tarbe shi yayin da ya ke dawowa daga masallacin Juma'a.
Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da rashawa ta jihar Kano ta bayyana kama wasu ma’aiakatan gwamnati guda biyu kan zargin sayar da takardun aiki ga mazauna jihar.
Babbar kotun tarayya mai zama a jihar Kano ta ce tana da hurumin sauraron karar da ta shafi tauye hakƙin Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero.
Gwamnatin Kano ta zargi tsohuwar gwamnatin da gazawa wajen inganta ilimi bayan ta samu dalibai miliyan 4.7 na zama a kasa babu kujeru a makarantunsu.
Iyalan Shehin Ɗarikar Tijjaniya, Sheikh Ibrahim Nyass sun buƙaci Muhammadu Sanusi II ya hakura da sarauta Kano, ya yi kori da kakansa Muhammadu Sanusi I.
Jihar Kano
Samu kari